NSCDC Ta Ba da Guraben Aiki Ga Iyalan Jami’anta 7 Da ’Yan Bindiga Suka Kashe
- Kwanaki kadan bayan kashe jami’anta bakwai, hukumar tsaro ta NSCDC ya ba da guraben aiki ga iyalansu
- NSCDC ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamatan, ta ba da kudade garesu don rage musu radadin rashi
- Rahoto ya bayyana yadda wasu tsagerun ‘yan bindiga suka hallaka jami’an tsaro da yawa a jihar Kaduna a makon jiya
Jihar Kaduna - Hukumar tsaro ta NSCDC a Najeriya ta ba da aiki kai tsaye ga iyalan wasu jami’anta bakwai da ‘yan bindiga suka kashe a jihar Kaduna.
An kashe jami’an tsaron bakwai ne a yayin wani harin da ‘yan bindiga suka kai a wata mahaka a kauyen Kuriga da ke karamar hukumar Birnin Gwari na jihar a ranar 10 ga watan Janairun baan.
Hakazalika, ‘yan bindigan sun hallaka wasu jami’an tsaro da ke tare na NSCDC a lokacin da suka kai farmakin.
Da yake magana da ahalin jami’an da suka mutu a Kaduna, kwamanda janar na hukumar, Ahmad Audi ya bayyana jimaminsa da samun labarin mutuwar yaransa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kuma bayyana cewa, wannan babban rashi ga ahalinsu da na kasar nan baki daya, kamar yadda rahoton Channels Tv ta tattaro.
Shugaban na NSCDC ya kuma ba d cekin kudi ga iyalan mamatan don rage musu radadi da jajanta musu.
An ba da guraben aiki ga iyalan mamayan
A bangare guda, ya sanar da guraben aiki ga iyalai ko dangin jami’an da suka mutu a matsayin diyya da cike gurbin mamatan.
Ya tabbatar musu cewa, hare-haren ‘yan bindiga ba zai karya gwiwar hukumar ba daga yin ayyukanta na wanzar da tsaro a Najeriya, Daily Post ta ruwaito.
Ya kuma bukaci jami’an hukumar da su ci gaba da kokari da jajircewa wajen tabbatar da tsaron kasar nan a manufarsu ta yaki da ta’addanci.
Sojoji Sun Fatattaki ’Yan Bindiga, Sun Sheke 2 a Karamar Hukumar Chikun
A wani labarin kuma, kunji yadda jami'an tsaro a Najeriya suka yi nasarar fatattakar 'yan bindiga tare da sheke wasu da yawa a Kaduna.
An ruwaito cewa, akalla 'yan bindiga biyu ne aka sheke tare da kwato babura da kayayyakin aikata laifuka munana.
Jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda masu kawowa kasar nan cikas.
Asali: Legit.ng