Zaben 2023: Gwamna Mai Karfin Fada A Ji A Arewa Ya Bawa Makarantu Hutun Kwana 8, Ya Bayyana Dalili
- Gwamnatin jihar Borno ta dauki muhimmin mataki don bawa mutanen jihar daman su yi zabe a watan Fabrairu
- Ma'aikatar ilimi na jihar Borno ta bada hutun kwana takwas ga dalibai da malamai don samun daman yin zabe
- A bangare guda, gwamnatin jihar Legas ita ma ta bada hutun kwana hudu don ma'aikatan gwamnati su samu daman karbar katin zabe na PVC
Jihar Borno - Gwamnatin Jihar Borno ta dauki muhimmin mataki don bawa mutanen jihar dama jefa kuri'a a zaben 2023 da ke tafe.
Ma'aikatar ilimi na jihar Borno ta bada hutun kwana takwas ga makarantu a jihar gabanin babban zaben 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnatin Borno ta bada hutun kwana takwas
A wata wasika mai dauke da sa hannun direkta na makarantu da ma'aikatar ilimi na jihar Borno, Mr Mustapha Umara, ya yi bayanin cewa hutun zai bada dama ma'aikata da dalibai da suka cancani yin zabe su sauke nauyin da ke kansu, rahoton The Punch.
Wasikar ta ce:
"Hutun kwana takwas din zai fara ne daga ranar Alhamis, 23 ga watan Fabrairu zuwa Laraba 1 ga watan Maris na 2023, don zaben shugaban kasa da majalisa da Alhamis 9 ga watan Maris zuwa Laraba 15 ga watan Maris na 2023 don zaben gwamna da yan majalisar jihar.
"Ana bukata dukkan makarantu su bi dokar sau da kafa."
Gwamnatin Jihar Legas ta bada hutun kwanaki hudu, ta bada dalili
Gwamnatin jihar Legas ta bada hutun kwana hudu ga ma'aikatan gwamnati don basu damar karbar katin zabe na PVC gabanin babban zaben 2023.
Shugaban ma'aikata, Hakeem Muri-Okunola ne ya sanar da hakan cikin wata takarda da ya fitar a ranar 18 ga watan Janairu.
Muri-Okunola ya ce Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya amince a bada hutun daga ranar Talata 24 ga watan Fabrairu zuwa Juma'a 27 ga watan Janairu ga matakai daban-daban na ma'aikatan gwamnati.
Gwamnan Borno Ya Yi Wa Bola Tinubu Alkawarin 95% Na Kuri'un Jiharsa A Zaben 2023
Farfesa Babagana Umara Zulum, gwamnan jihar Borno ya yi alkawarin ba wa jam'iyyar APC kuri'u 95 cikin dari a zaben 2023.
Zulum ya yi wannan alkawarin ne ga matar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu yayin tattaunawa da tawagar kamfen din mata a Borno.
Asali: Legit.ng