Fafutukar Neman Ma'adai Ne Ya Haddasa Matsalar Tsaro a Arewa, Kwankwaso

Fafutukar Neman Ma'adai Ne Ya Haddasa Matsalar Tsaro a Arewa, Kwankwaso

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP ya bayyana abinda ya kawo ayyukan ta'addanci arewacin Najeriya
  • Da yake jawabi a Landan, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce matsalar ta samo asali ne daga faɗa kan Gwal da sauran ma'adanan yankin
  • Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa mutane daga ciki da wajen Najeriya ne suke sace ma'adanan

London, United Kingdom - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso, yace fafutukar neman ma'adan kasa ne asalin abinda ya haifar da ta'addanci a arewa maso yamma da arewa maso gabas.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a Chatham House da ke birnin Landan na ƙasar Burtaniya ranar Laraba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Rabiu Musa Kwankwaso.
Fafutukar Neman Ma'adai Ne Ya Haddasa Matsalar Tsaro a Arewa, Kwankwaso Hoto: Rabiukwankwaso
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Ministan tsaro yace mutane daga ciki da wajen Najeriya ke "Satar" ma'adanai shiyasa yaƙi ya turnuke yankunan.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

A jawabinsa, Kwankwaso ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A ƙasata Najeriya muna da tsarin lada da kuma tsarin hukunci saboda a halin yanzun komai ya wuce. Lokacin ina gwamnan Kano, ba wanda zai je da sunan gwamnati ya karbi harajin ƙwandala ɗaya."
"Tsawon shekaru 8 da na kwashe kan madafun iko ban karbo bashin ko kwabo ba, abinda muka maida hankali shi ne albarkatun jiharmu, shiyasa wasu mutane ke tambayar wai ina muke samun kuɗin shiga."
"Yaƙe-yaƙen da ake a arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya duk kan ma'adanan ƙasa ne, mutane na sace su daga cikin Najeriya da waje, ciki harda Gwal da sauran ma'adanai."

Kwankwaso ya ce lokacin ya yi da wannan matsalar zata kau, gwamnati ta ƙwace wadannan Arzikin da Allah ya bamu domin yi wa yan kasa aiki.

Bugu da kari, tsohon gwamnan yace Najeriya ta wayi gari cikin wannan bakin yanayin ne sakamakon gurbataccen shugabanci da kuskuren zabe, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ba Wanda Zai Ci Bulus: Atiku Ya Gindaya Sharadin Baiwa Mambobi da Manyan PDP Mukami Idan Ya Ci Zabe

Zan iya hakura da takara amma ka sharadi 1 - Kwankwaso

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, yace abu ɗaya zai sa ya janye daga neman takarar shugaban kasa a 2023

Da yake jawabi a Landan, Ɗan takara a inuwar NNPP ya ce idan har akwai wanda ya fi shi cancanta to zai hakura ya bar masa.

Kwankwaso na ɗaya daga cikin manyan yan takara hudu da ake hasashen ɗayansu ne zai karbi mulkin Najeriya a 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262