Yan Sanda Sun Ceto Matashiyar da Aka Sace a Katsina Bayan Sa’o’i 24 a Tsare
- Jami'an rundunar yan sanda a jihar Katsina sun ceto daya daga cikin matan da yan bindiga suka sace a hanyarsu ta zuwa coci a karamar hukumar Kankara
- An ceto Alhakatu Shuaibu mai shekaru 13 awanni 24 bayan faruwar lamarin a ranar Litinin, 16 ga watan Janairu
- Gwamna Aminu Masari ya umurci hukumomin tsaro a jihar da su gaggauta ceto matan da aka sace a ranar Lahadi
Katsina - Rundunar yan sandan jihar Katsina ta ce ta ceto wata matashiya yar shekaru 13, Alhakatu Shuaibu wacce yan bindiga suka sace tare da sauran masu bauta a karamar hukumar Kankara da ke jihar.
Da yake tabbatar da ci gaban ga jaridar The Cable, kakakin yan sandan jihar, Gambo Isah ya ce an ceto yarinyar ne a ranar Litinin, 16 ga watan Janairu.
Ya ce an kai ta babban asibitin Kankara don samun kulawar likitoci kuma tuni aka mika ta ga iyayenta.
Mun dai ji cewa yan bindiga sun farmaki cocin New Life for Alla da ke garin sannan suka yi garkuwa da masu bauta yayin da suke hanyarsu ta zuwa bauta a coci ranar Lahadi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ba a harbi limamin cocin ba an dai ji masa rauni
Isah ya ceba a harbi faston ba amma dai na samu karaya bayan an doke shi da katako a kafadunsa.
Ya ce:
"Mutanen da aka sace mata ne su bakwai. Biyu daga cikinsu na da yara kanana biyu. An dauki faston zuwa babban asibitin Kankara, an masa magani.
"An bugi faston da katako a hannunsa kuma ya samu karaya sakamakon haka. Ba harbin bindihga bane kamar yadda aka rahoto da farko.
"An ceto yarinyar mai shekaru 13, Alhakatu Shuaibu washegarin ranar, wato Litinin kenan. An dauke ta zuwa asibiti kuma an bata kulawa. Tuni aka sada ta da iyayenta."
Kakakin yan sandan ya bayar da tabbacin cewa rundunar na hada kai da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da ceto sauran mutanen da aka sace a jihar.
Ya kara da cewa:
"Yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji, sojojin sama, DSS da civil defense na aiki kai da fata don ceto sauran mutanen."
Gwamna Masari ya umurci hukumomin tsaro su gaggauta ceto matan
A halin da ake ciki, Gwamna Aminu Bello Masari ya umurci hukumomin tsaro a jihar Katsina da su tabbatar da ceto matan Kirista tara da yan bindiga suka sace a hanyarsu ta zuwa coci a ranar Lahadi a karamar hukumar Kankara, rahoton Vanguard.
Kan haka, gwamnatin Masari ta ce ta yi Karin yan bijilanti 1,900 da aka horar kuma za a tura su yankunan don magance rashin tsaro.
Asali: Legit.ng