Wata Mota Dauke Da Jarkokin Man Fetur Da Kama Da Wuta A Kano

Wata Mota Dauke Da Jarkokin Man Fetur Da Kama Da Wuta A Kano

  • Wata mota kirar sharon ta yi gobara a kofar fita daga gidan man fetur na NNPC da ke Murtala Mohammed Way Kano
  • Wani ganau ya bayyana cewa motar da ta kama da wutan tana shirin fita daga gidan man ne bayan an cika ta da jarkokin man fetur
  • Rahotanni sun bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar da motar ta yi amma direban motar ya samu karamin rauni

Jihar Kano - Wata mota kirar Sharon dauke da man fetur a cikin jarkoki ta kama da wuta a kofar shiga gidan man fetur na NNPC da ke Club Road, Murtala Mohammed Way a Kano.

A cewar wasu wadanda abin ya faru a idonsu, motar ta kama da wuta ne a yayin da ta ke shirin barin gidan man misalin karfe 5 na yammacin ranar Talata.

Kara karanta wannan

2023: Dubbannin 'Yan SPW Sun Yanke Shawara, Sun Fadi Wanda Zasu Goyi Baya Tsakanin Tinubu da Atiku

Mota ta kama da wuta
Wata Mota Dauke Da Man Jarkokin Fetur Da Kama Da Wuta A Kano. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Ba a rasa rai ba sakamakon gobarar

Daily Trust ta gano cewa babu wanda ya rasa ransa sakamakon lamarin, amma direban motar ya samu karamin rauni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan 'Black Market' aka fi sayar wa man fetur a gidan man, Ahmad

Jafar Mohammad Ahmad wanda aka fi sani da Sanjo Badawa, wanda ya yi magana da wakilin majiyar Legit.ng ya ce:

"Maganar gaskiya, akwai masu babura fiye da 300 a cikin gidan man, sun ki sayar mana da mai. Kawai wadannan yan bunburutun (black market) suke sayarwa.
"Mota daya za ta siya man fetur kimanin na N50,000 ita kadai hakan kuma yana bata lokaci. Sun kawo man misalin karfe 11 na safe amma sun fara sayarwa misalin karfe 5 na yamma."

An yi asarar dukiyoyi sakamakon gobarar da ta faru a hedkwatar yan sanda na Kano

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gidan Man AA Rano da Tankar Dakon Fetur Sun Kama da Wuta a Abuja

Kun ji cewa an yi gobara wacce ta kone kayayyaki na miliyoyi sakamakon wuta da ta tashi a hedkwatar yan sanda da ke Bompai, karamar hukumar Nasarawa a Kano.

Daily Sun ta rahoto cewa wutar ta fara ci ne misalin karfe biyu na ranar Asabar 14 ga watan Janairun shekarar 2023.

Wani shaidan gani da ido ya ce wutar ta fara ne daga ofishin Provost sannan ta bazu zuwa wasu ofisoshin ciki har da na PRO da wasu jami'an.

Sai dai daga bisani ma'aikatan kwana-kwana na jihar Kano sun iso wurin kuma sun samu nasarar kashe gobarar yayin da jami'an tsaro suka zagaye wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164