An Shiga Damuwa Yayin da Shahararren Gwamnan APC Ya Kamu da Rashin Lafiya, Gwamnati Ta Yi Karin Haske

An Shiga Damuwa Yayin da Shahararren Gwamnan APC Ya Kamu da Rashin Lafiya, Gwamnati Ta Yi Karin Haske

  • Gwamnatin jihar Ondo ta fayyace gaskiyar lamari a kan halin da lafiyar Gwamna Rotimi Akeredolu ke ciki
  • Richad Olatunde, babban sakataren labaran gwamnan, ya bayyana cewa babu wani abun tayar da hankali domin dai gwamnan na samun sauki daga rashin lafiyar da ke damunsa
  • Olatunde ya jaddada cewar kariyar da ofishin gwamnan ke da shi bai hada da na lafiyarsa ba cewa Akeredolu na aiwatar da aikinsa kamar yadda ya kamata

Ondo - Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo ya yi karin haske a kan halin da lafiyarsa take ciki a ranar Talata, 17 ga watan Janairu.

Halin da gwamnan ke ciki ya haifar da damuwa a jihar amma sanarwar da Richad Olatunde, sakataren Akeredolu ya fitar ya bayyana cewa babu wani abun tashin hankali, jaridar This Day ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Ɗan Takarar Jam'iyyar PDP a 2023 Ya Kwanta Rashin Lafiya, Gwamna Ya Magantu

Rotimi Akeredolu
An Shiga Fargaba Yayin da Shahararren Gwamnan APC Ya Kamu da Rashin Lafiya Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi
Asali: Facebook

Gwamnatin Ondo ta bayyana ainahin halin da Gwamna Rotimi Akeredolu yake ciki

Olatunde ya ba mutanen jihar Ondo da yan Najeriya baki daya tabbacin cewa gwamnan na cikin yanayi mai kyau kuma kada a tayar da hankali.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jawabin ya bayyana cewa gwamnatin jahar ba za ta iya biris da damuwar da mutane ciki ba yayin da ya bayyana cewa da izinin Allah, babu wani abun tayar da hankali game da lafiyar Akeredolu.

Olatunde ya bayyana cewa gwamnan bai da banbanci da sauran mutane yayin da ya kara da cewar yana samun sauki daga rashin lafiyar da yake fama da ita.

Wani bangare na jawabin na cewa:

"Gwamnan dan adam ne kuma kariyar da ofishinsa ke da shi bai shafi lafiyar jikinsa ba, don haka wannan ba sabon abu bane."

Jawabin ya kuma jaddada cewar lafiyar gwamnan ba kamar yadda ake ta yayatawa bane domin Akeredolu na aiwatar da aikinsa kamar yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Da Gaske ICPC Ta Kama Dan Takarar Gwamnan APC a Sokoto Kan Badakalar Biliyan N12? Aliyu Sokoto Ya Fayyace Gaskiyar Lamari

Atiku ya kai ziyara jihar Filato don ta'aziyyar mambobin PDP da suka mutu a hatsarin mota

A wani labari na daban, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 30 ga magoya bayansa da hatsarin mota ya ritsa da su a jihar Filato.

Atiku wanda ya dakatar da harkokin siyasarsa don zuwa yiwa al'ummar Filato ta'aziyyar rashin da suka yi, ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng