Peter Obi Zai Kai Ziyara Arewa, Zai Gana da Shugabannin Addinai da Sarakuna a Jihar Kaduna
- Jihar Kaduna za ta yi babban bako, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour zai kus-kus da malaman addini
- Hakazalika, rahoto ya ce Peter Obi zai zauna da Sarkin Zazzau da na Jema'a duk dai a jihar ta Kaduna da ke Arewa maso Yamma
- Peter Obi na ci gaba da fadada takararsa da neman goyon bayan manyan mutane a yankin Arewacin Najeriya da Kudancinta
Jihar Kaduna - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi zai yi zaman tattaunawa da shugabannin addinai a yankin Kaduna ta Kudu, kana zai ziyarci sarakuna a yankin.
Hakazalika, Obi zai gudanar da wani taron gangami a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna, inda zai gana da dalibai daga makatrantu daban-daban da kuma ‘yan a mutun jam’iyyar da magoya bayansa.
Wannan na fitowa ne daga bakin kakakin jam’iyyar, Dr Yunusa Tanko a yayin wata gwarya-gwaryar zama a jihar Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.
Obi zai gana da Sarkin Zazzau da na Jema'a
Ya kuma bayyana cewa, Obi zai kai ziyara zuwa fadar Sarkin Zazzau, Amb, Ahmad Nuhu Bamalli da kuma Sarkin Jema’a a Kafancan da ke yankin Kudancin jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dr Tanko ya kuma bayyana cewa, a yayin taron na kamfen, Obi zai karanto manufofinsa bakwai da yake son cimmawa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben bana.
Peter Obi na ci gaba da tallata kansa da manufofinsa ga ‘yan Najeriya, hakazalika, yakan fadi maganganu da nuna nagarta da kwarewarsa a mulki.
Obi ya sha bayyanawa ‘yan Najeriya cewa, shi ya cancanci ya gaji Buhari a zaben bana, lamarin da ke kara daukar hankali a kasar.
A tun farko, ya dauko abokin takararsa daga Arewacin Najeriya kuma dan jihar Kaduna, Dr Datti Baba-Ahmed.
Asali: Legit.ng