Dandazon Jama’a Sun Taru a Nasarawa, Sun Yi Haba-Haba da Zuwan Kwankwaso Na NNPP
- Dan takarar shugaban kasa a jamiyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya lashe zukatan mutan Arewa ta tsakiya
- Jagoran na siyasa ya dura jihar Nasarawa, inda dandazon jama'a suka bayyana goyon bansu gare shi gabanin zaben shugaban kasa
- A baya ya samu irin wannan marawar baya a ga mutanen yankin Arewa maso Gabas, dandazon jama'a sun taru
Lafia, jihar Nasarawa - A ci gaba da taron gangamin kamfen da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ke yi a Najeriya, ya shilla jihar Nasarawa domin kaddamar da kamfen dinsa a yankin Arewa ta tsakiya.
Tawagar gangamin nasa da shi kansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun yi taro a jiya Litinin 16 ga watan Janairun 2023 a birnin Lafia ta jihar Nasarawa.
Taron ya samu halartan dubban jama'a daga yankuna daban-daban na yankin Arewa ta tsakiya a Najeriya.
A wani sako da kafar Kwankwasiya Reporters ta yada, ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Jam'iyyar NNPP na ci gaba da gangaminta na zaben 2023 a shiyyoyin kasar nan.
"Jam'iyyar ta yi taron gangamin kamfen dinta a Arewa ta tsakiya a Lafiya, jihar Nasarawa a yau (16 ga watan Janairu, 2023)."
Kalli hotunan:
Nasarawa tawa ce, inji Kwankwaso
Da yake yaba irin tarbar da ya samu a jihar ta Nasarawa, Kwankwaso ya ce tabbas ya shaida cewa jihar Nasarawa ta shi ce, kuma ana goyan bayansa.
Hakazalika, ya mika godiya da jin dadinsa bisa ganin dandazon jama'ar da suka yi masa kyakkyawar tarba a jihar.
"Nagode, Jihar Nasarawa. Yau shaida ne cewa ku ne NNPP, mun gode da irin misali da kuka buga na nuna goyon baya da kauna. RMK."
Jam'iyyun siyasa a fadin kasar nan na ci gaba da tallata 'yan takararsu gabanin zaben shugaban kasa da ke tafe nan da wata guda.
Kwankwaso Ya Sha Alwashin Mai da Wa’adin Sakamakon JAMB Ya Koma Tsawon Shekaru 4
A wani labarin kuma, kunji yadda Kwankwaso ya sha alwashin kawo sauyi a fannin ilimi a Najeriya, farawa daga hukumomin shirya jarrabawa.
Dan takarar ya ce, zai mai da wa'adin lalacewar sakamakon jarrabawar JAMB ta zama shekaru hudu saboda ba dalibai a Najeriya damar shiga jami'a.
Ya bayyana hakan ne a taron gangamin NNPP da aka gudanar a yankin Arewa maso Gabas a kwanan nan.
Asali: Legit.ng