Jami’in da Ke da Hannu a Kisan Raheem Bolanle Ya Musanta Aikata Laifin Kisa
- Bayan gurfanar da dan sandan da ya kashe wata lauya mai juna biyu a Legas, ya musanta laifin da ake zarginsa dashi
- Drambi Vandi ya musanta zargin ne a gaban kotu a yau Litinin 16 ga watan Janarun 2023, inji rahotanni
- A baya rahoto ya bayyana yadda dan sandan ya dauki bindiga ya bindige wata mata da ke kan hanyar dawowa daga coci ranar Kirsimeti
Jihar Legas - Drambi Vandi, dan sandan da ake zargi da bindige wata mata lauya mai juna biyu a jihar Legas mai suna Raheem Bolanle ya musanta laifin da ake zarginsa dashi.
An gurfanar da Vandi ne a ranar Litinin a gaban wata babbar kotun jihar Legas da ke zama a Tafawa Balewa Sqaure (TBS) tare da bayyana tuhumarsa da kisan lauyar.
Bayan da aka karanta masa laifinsa, Vandi ya ce sam bai aikata laifin kisa ba, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.
Yadda lamarin ya faru tun farko
Idan baku manta ba, a ranar 25 ga watan Disamban bara ne ASP na ‘yan sanda ya dirkawa matar bindiga a lokacin da take kan hanyar dawowa daga ibadar kirsimeti.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan lamari dai ya faru ne a yankin Ajah na jihar ta Legas, kuma ya jawo cece-kuce mai daukar hankali.
Mutane da yawa a Najeriya sun bayyana bacin rai da samun labarin mutuwar Bolanle, ciki har da manyan masu fada a ji a fannin siyasa.
Daga nan ne sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya ya ba da shawarin dakatar da Vandi tare da gurfanar dashi a gaban kotu.
An dakatar da dan sandan da ya sheke lauya mai juna biyu
Daga nan hukumar aikin ‘yan sanda ta PSC ta amince da shawarin tare da dakatar da jami’in a ranar 29 ga watan Disamban bara, Punch ta ruwaito.
A ranar 30 ga watan, gwamnatin jihar Legas ta shigar da kara kan Vandi tare da tuhumarsa da aikata kisan kai.
Ya zuwa lokacin zaman shari’ar, an tsare Vandi ne a gidan gyaran hali na Ikoyi, kamar yadda rahotanni suka bayyana a baya.
A bangare guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya ta bayyana damuwa game da yadda hukumar ‘yan sanda ke tafiyar da lamarin.
IGP dai ya nuna hukumar 'yan sanda ba ta goyon bayan irin wannan mummunan aiki na kisan fararen hula da bata-garin 'yan sanda ke yi.
Asali: Legit.ng