Yanzu Yanzu: Shahararren Jarumin Nollywood Papa Ajasco Ya Mutu

Yanzu Yanzu: Shahararren Jarumin Nollywood Papa Ajasco Ya Mutu

  • Fitaccen jarumin wasannin barkwanci na kudu, Femi Ogunrombi wanda aka fi sani da Papa Ajasco, ya kwanta dama
  • Mai ruwa da tsaki a harkokin wasan kwaikwayo, Husseini Shaibu, shi ya sanar da labarin mutuwar jarumin a ranar Lahadi
  • Jarumin ya yi suna sosai a lokacin da yake raye saboda rawar ganin da ya taka a cikin shiri mai dogon zango wato Papa Ajasco

Shahararren jarumin masana'antar shirya fina-finai na Nollywood, Femi Ogunrombi wanda aka fi sani da Papa Ajasco ya mutu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Wani na kusa da masana'antar shirya fina-finan kuma lakcara, Husseini Shuaibu ne ya sanar da labarin mutuwarsa a wata wallafa da ya yi a shafin Twitter a ranar Lahadi, 15 ga watan Janairu

Papa Ajasco
Yanzu Yanzu: Shahararren Jarumin Nollywood Papa Ajasco Ya Mutu Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya rubuta a shafiunsa:

"Yanzun nan na samu labarin cewa shahararren mai kida, tsohon mai koyar da waka a kamfanin NATIONALTROUPE kuma jarumin da ya taba fiowa a matsayin 'Papa Ajasco' a cikin shirin barkwanci na @waleadenugaprod ‘Papa Ajasco’, Mista Femi Ogunrombi ya MUTU."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tsohon Daraktan Kamfen Shugaban Kasa Ya Magantu Bayan DSS Ta Cafke Shi a Filin Jirgi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Takaitaccen tarihin Marigayi Papa Ajasco

Femi Ogunrombi ya karanci fannin waka da dirama a jami'ar Obafemi Awolowo. Ya kasance malamin waka, wai hada kida, jarumi, furodusa kuma daraktan waka da fim.

Yayin da yake jami'ar OAU, ya kafa wata kungiya ta mawaka mai suna The Ayoro Voices. Wannan kungiya ita ke fito al'adun jami'ar tsakanin 1980 da 1983.

A 1994, Femi ya shiga kungiyar mawaka ta kasa a matsayin mai koyar da waka karkashin ma'aikatar labarai da al'adu.

A 1998, ya tashi zuwa matsayin daraktan waka, sannan ya kafa kungiyar mawaka ta kasa. A 1998, ya bar aikin gwamnati don gudanar da nasa kasuwancin wakar.

Barinsa aikin gwamnati yasa ya zama mai bayar da shawara ga gwamnatocin jihohi daban-daban a fadin kasar.

Ya yi aiki da kwamitin wasanni da al'adu na jihar Lagas karkashin Cif Misis Idowu Shonubi a 1999 zuw 2002. Sai kuma kwamitin wasanni da al'adu na jihar Ekiti karkashin Misis Yetunde Fosudo a 2014.

Kara karanta wannan

Shahararren Mawakin Najeriya Zai Daina Waka, Zai Zama Makarancin Kur’anin Duniya

Marigayin ya kuma yi aiki a matsayin mai bayar da shawara ga kwamitin wasanni da al'adu na jihar Kuros Riba karkashin Marigayi Bassey Effiong.

A wani labari na daban, mun ji cewa jama'a sun cika da mamaki bayan ganin bidiyon wani mutum da ya yi kama da shugaban kasa Muhammadu Buhari yana tafiya a hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng