Goodluck Jonathan: Muna Makancewa Idan Mun Samu Mulki Na Siyasa

Goodluck Jonathan: Muna Makancewa Idan Mun Samu Mulki Na Siyasa

  • Goodluck Jonathan, tsohon shugaba kasar Najeriya ya shawarci yan siyasa kan bari giyyar mulki na bugar da su
  • Dattijon kasar ya yi wannan gargadin ne yayin wani taro da aka yi don murnar murabus din alkaliyar alkalai na jihar Bayelsa, Mai shari'a Kate Abiri
  • Sanata Douye Diri, gwamnan Bayelsa shima ya yaba wa Abiri bisa hidimar da ta yi wa bangaren shari'a yana mai cewa ko bayan murabus jihar za ta bukaci ayyukanta da shawarwari

Yenagoa - Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi nasiha yan siyasa su kyalle bangaren siyasa su rika yin ayyukansu da doka ta tanada, yana mai cewa idon yan siyasa na rufewa idan sun samu mulki.

Jonathan ya yi wannan nasihar ne yayin gabatar da wani littafi da aka shafe sati daya ana yi don bikin murabus din alkaliyar alkalan jihar Bayelsa, Mai shari'a Kate Abiri, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Zagaye Mai Kama Da Shugaba Buhari a Wani Bidiyo Da Ya Yadu

Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan: Muna Makancewa Idan Mun Samu Mulki Na Siyasa. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wurin taron a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, Jonathan ya yaba muhimmin rawar da Mai shari'a Abiri ta taka lokacin da ta rantsar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ta kawar da rikicin kundin tsarin mulki a jihar, rahoton LIB.

Muna makancewa idan mun samu mulki na siyasa, Jonathan

Ya shawarci yan siyasa kada su rika bari giyan mulki ya rika rudarsu, yayin da ya yi kira ga alkalai su tabbatar suna adalci da rashin tsaro yayin tabbatar da shari'a.

Ya ce:

"Ina bada shawara ga yan siyasa cewa a lokacin da muke mulki, kada mu yi kokarin yin barazana da bangaren shari'a domin ra'ayin yan mazan jiya gare su. Idan muka samu iko na siyasa, mu kan makance. Ya kamata yan siyasa su sani cewa al'umma tana canjawa.

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: DPO ya Yanke Jiki Ya Fadi a Ofishinsa, Ta Rasu a Take

"Yau, muna taya alkalin alkaliyar mu murna saboda ta yi hidima na gari. A 2015, ta bar Bayelsa zuwa Ribas don rantsar da gwamna don kawar da tabarbarewar doka da oda. Kamar bangaren shari'a ya fi na zartarwa aiki."

Jawabin gwamnan Bayelsa

A yayin jawabinsa, Sanata Douye Diri, ya jinjinawa mai shari'a Abiri bisa nasarorin da ta samu, yana mai cewa cikin aikinta na shekaru 15 a matsayin alkaliyar alkalai, ta rantsar da gwamnoni uku a Bayelsa da daya a Ribas.

Sune Cif Timipre Sylva (2008), Sanata Seriake Dickson (2012), Sanata Douye Diri (2020) da Nyesom Wike (2015).

Gwamna Diri ya bayyana Abiri a matsayin abin koyi ga sauran alkalai wacce ta yi hidima na shekaru 30 ga bangaren shari'a.

Ya ce har yanzu jihar za ta bukaci ayyukanta saboda jajircewarta da kwarewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164