Zan Kawar Da Tsadar Rayuwar Da Aka Kakabawa Yan Nigeria Idan Suka Zabe Ni
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu yace al'ummar Nigeria su sha kuruminsu indai sun zabeshi
- Matsalar tsadar rayuwa, matsalar fetir da duk wata matsala da take ciwa yan Nigeria tuwo kwarya tazo karshe in aka dangwalamin
- Kwanaki arba'in da biyu ne ya rage a kada kuri'a a babban zaben Nigeria, inda za'a zabi shugaban kasa da gwamnoni hadi da yan majalissar kasa, jiha dana dattijai
Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ikirarin magance matsalar tsadar rayuwa da aka kakabawa yan Nigeria, karancin mai, Matsalar tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki in aka zabe shi.
Tinubu na fadin hakan ne yayin da yake kaddamar da shirin kan tattalin arziki a wabi taro da hadakar zauren ci gaban tattalin arzikin Nigeria NESG suka shirya.
"In kana san samun nasara kan tattalin arziki, dole ne sai ka magance matsalar tsaro, satar mutane, sabida ba kasar da zata ci gaba ba tare da magance wannan matsaltsalun ba"
"Abinda na yarda da shi shine, bangarorin dana ba gwamnati ba suna taimakawa sosai wajen habaka tattalin arziki, shi yasa gwamnati ta tsara yadda bangarorin da bana gwamnati ba zasu tafikar da aiyukansu kamar yadda kuka sani" Tinubu ya fada
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa an jiyo mai magana da yawunsa na cewa gwamnatinsa, zata tabbatar da samun dai-daito a tsakanin yan kasa kan hada-hadar kudi, samar da kayan gida, samar da aiyukan yi da bunkasa yanayin siye-da-siyarwa a fadin kasar.
Magance hauhawar farashi da tsadar rayuwa
Domin magance matsalar tattalin arziki, da matsi da sauransu, dole sai ka bi wasu sharuda wajen dakatar da hauhawar farashi, matsalar mai, da kuma wasu tsaruka kan hada-hadar kudi
"Ni ban ga ga dalilin da zai sa ace ana son habaka tattalin arziki ko sauwakawa yan kasa kuma ace baza magance wadannan matsalolin ba, duba da yadda suke."
Kan batun cire tallafin mai kuwa, Bolan yace:
"Shawarace da da tunani mai kyau kan cewa sai mun cire tallafin mai nan take, sabida samawa al'umma mafita, sabida baza mu ci gaba da taimakawa kasashen da muke mkwabtaka da su ba."
Tinubu yace gwamnatinsa zatai kasafi ne kan abunda takeyi da kuma kashewa, sabida tana so ta bunkasa tattalin arzikin da kashi gonma da kuma rage rashin aikin yi, dan habaka tattalin arzikin Nigeria.
Asali: Legit.ng