Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo Ya Bada Wasu Shawarwari Masu Dauke Da Hikima Ga Shugaban Najeriya Na Gaba

Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo Ya Bada Wasu Shawarwari Masu Dauke Da Hikima Ga Shugaban Najeriya Na Gaba

  • An bukaci yan Najeriya su tabbatar sun zabi shugaban kasa wanda ya fahimci yadda tattalin arzikin kasar ya ke
  • Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ne ya yi wannan kirar a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu
  • Obasanjo ya ce duk wanda zai gaji Shugaba Buhari, dole ya ciyar da Najeriya gaba daga matakin masu tunani zuwa masu aiwatar da aiki

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu, ya lissafa wasu muhimman abubuwa da ya zama dole shugaban kasa na gaba ya duba su.

The Nation ta rahoto cewa yayin jawabin da Obasanjo ya yi wano taro da aka yi ta kafar intanet da Africa Leadership Group ta shirya, ya ce dole shugaba na gaba ya magance manyan kallubalen da kasar ke fuskanta bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Shekaru 15 Bayan Barin Mulki, Obasanjo Ya Fadi Abin da Ya Hana Shi Yin Tazarce Sau 2

Obasanjo
Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo Ya Bada Wasu Shawarwari Masu Dauke Da Hikima Ga Shugaban Najeriya Na Gaba.
Asali: Instagram

Ya kara da cewa dole shugaba na gaba ya kawo karshen kallubale kamar ta'addanci, yan bindiga, da garkuwa da mutane a jihohin kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dage Najeriya sama daga matakin kasashe masu tunani kawai

Obasanjo ya ce dole Najeriya a matsayinta na kasa ta yi kokarin wuce matakin tunani kawai ta zama mai aiwatarwa domin cimma wannan nasarorin.

Kalamansa:

"Ina fatan mutumin da zai zama shugaban kasa na gaba, zai zama irin shugaba ne wanda zai fahimci tattalin arziki, wannan na da muhimmanci.
"Idan ya fahimci tattalin arziki, akwai abubuwa da ya zama dole ya yi; yin wani abu kan tallafin man fetur. Kuma, bashin kasar bai da kyau, dole a yi wani abu kansa.
"Adadin man fetur da ake sacewa a kasar abu ne mai dore kai. Rashawa da ake yi a wasu sassan shima abin damuwa ne. Kuma, yan bindiga, da garkuwa sun zama ruwan dare."

Kara karanta wannan

Bishop Kukah Ya Magantu, Ya Fadi Abun da Babban Hadimin Buhari Ya Fada Masa Bayan Ya Caccaki Fadar Shugaban Kasa

An gano dan takarar shugaban kasa da Obasanjo ya ke goyon baya a zaben 2023

A wani rahoton, bayan lokaci mai tsawo ana ta hasashe, daga karshe an gano dan takarar shugaban kasa da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ke goyon baya a 2023.

Akin Osuntokun, sabon darakta janar na kwamitin yakin neman zabe na jam'iyyar LP, ya ce Obasanjo yana goyon bayan Peter Obi.

Osuntokun ya ce tsohon shugaban kasar yana goyon bayan dan takarar shugaban kasar na LP dari bisa dari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164