Gwamnan bankin CBN, Emefiele Ya Dawo Najeriya a Asirce Saboda Gudun a Cafke Shi
- Gwamnan babban bankin Najeriya watau CBN ya shigo Najeriya bayan shafe makonni yana ketare
- Ana cewa Godwin Emefiele ya dawo kasar nan a boye ne domin yana gudun jami’an tsaro su cafke shi
- Idan labarin da aka samu ya tabbata, Emefiele ba zai dade ana Najeriya ba, zai sake lulawa kasar waje
Abuja - Ana kishin-kishin cewa Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN, Godwin Emefiele ya dawo Najeriya amma ba tare da jama’a sun sani ba.
Godwin Emefiele ya shigo kasar nan ne a asirce a ranar Larabar nan saboda yana tsoron jami’an tsaro su kama shi, Premium Times ta kawo rahoto.
Mista Godwin Emefiele ya bar Najeriya ne tun a makonnin baya da jami’an tsaro suka taso shi a gaba da zargin rashin gaskiya da taimakawa ta’addanci.
Wata Sabuwa: Hadimin Gwamnan PDP Ya Yi Fatali da Atiku, Ya Fadi Dan Takarar Da Yake Goyon Baya a 2023
Ana haka sai jami’an DSS suka nemi damar cakfe Gwamnan na CBN, amma kotu ta hana su ta karar da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/2255/2022.
Godwin Emefiele ya tafi hutu
Wata majiya ta ce Gwamnan babban bankin ya nemi izinin samun hutu na makonni biyu wajen shugaba Muhammadu Buhari, kuma an amince masa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Majiyar tace a ranar Talatar nan hutunsa ya kare, saboda dole Emefiele zai dawo aiki a ranar Laraba.
Amma jaridar ta samu labarin cewa duk da haka Gwamnan na CBN yana shirin sake fita daga Najeriya domin jami’an tsaro za su iya neman cafke shi.
“Yana shirin barin Najeriya nan da ‘yan kwanaki da sunan zai halarci taron majalisar tattalin arziki na Duniya.”
- Majiya
Da aka nemi jin ta bakin Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Garba Shehu a game da kitimurmurar gwamnan bankin, Punch tace ba a dace ba.
Ba a samu Kakakin babban bankin Najeriya, Osita Nwanisobi domin jin abin da zai fada ba. Har zuwa yau ana tunanin ana wasan boye-boye da gwamnan.
Emefiele ya shiga uku
A ‘yan kwanakin nan, Emefiele yana ta shan suka a dalilin tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya.
Ana haka sai ga shi ya shiga jam’iyyar APC yana neman zama ‘dan takaran shugaban kasa, alhali ba a san gwamnonin CBN da shiga harkar siyasa ba.
Za mu karbe Benuwai - APC
Rahoto ya zo cewa Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu yana ganin sauya-shekar da Gwamna Samuel Ortom tamkar sace masu kuri'ar 2015 ne.
Mu’azu Bawa Rijau ya wakilci shugaban APC wajen bikin kaddamar da yakin neman zaben APC a karamar hukumar Gboko, yace dole ne su karbe Benuwa.
Asali: Legit.ng