Kaka Da Jikanta Da Aka Tsare A Gidan Yari Kan Satar Kaji 2 Sun Shaki Iskar Yanci

Kaka Da Jikanta Da Aka Tsare A Gidan Yari Kan Satar Kaji 2 Sun Shaki Iskar Yanci

  • Alkalin alkalan jihar Oyo, Mai shari'a Munta Abimbola, ya saki wata dattijuwa yar shekara 65 da jikanta dan shekara 15 da ake tsare da su kan zargin satan kaji guda biyu
  • Mai shari'a Abimbola ya ce an saki kakan da jikanta ne sakamakon afuwa da aka musu saboda yawan shekarunta da rashin lafiya sannan jikanta yaro ne wanda bai balaga ba
  • Ma'aikatar shari'ar ta jihar Oyo karkashin jagorancin alkalin alkalan sunyi wannan afuwar ne ga mutanen da ake tsare da su kuma gabanin shari'a amma suna da kallubalen rashin lafiya, yawan shekaru da tsawon zama a gidan yarin

Jihar Oyo - Wata dattijuwa yar shekara 65 da jikanta dan shekara 15 sun yi murna bayan da kotu ta sake su daga gidan yari inda aka tsare da su kan zargin satan kaji biyu, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Kashe Yan Bijilante 3 A Wata Jihar Najeriya

Mai shari'a Munta Abimbola, alkalin alkalan jihar Oyo ya saki su yayin da suke jiran shari'a a gidan gyaran hali na Abolongo kan afuwa.

Taswirar Jihar Oyo
Kaka Da Jikanta Da Aka Tsare A Gidan Yari Kan Satar Kaji 2 Sun Shaki Iskar Yanci. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dattijuwar da jikanta suna tsare a gidan gyaran halin tun watan Disamban 2022 suna jiran shari'a.

An yi zargin cewa yaron ya sace kaji biyu ya kuma bawa kakansa don ta ajiye masa.

Mai shari'a Abimbola ya ce sun cancanci afuwa saboda yaron bai balaga ba kuma dattijuwar ta tsufa gashi bata da cikakken lafiya.

Ya gargade su kada su sake su koma yin sata ko kuma karbar kayan sata, The Eagle Online ta rahoto.

Alkalin alkalan Jihar Oyo ya bayyana dalilin sakin wasu mutanen da ake tsare da su a Oyo

Alkalin alkalan ya kuma saki wasu mutane 72 da ake tsare da su suna jiran shari'a.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Halaka Magidanci Tare da Sace Yaransa 2 a Farmakin da Suka Kai FCT

Mai shari'a Abimbola ya ce atisayen na afuwan an aiwatar da shi ne bisa shawarwarin kwamitin zartar da shari'a na jihar Oyo karkashin jagorancinsa.

Ya ce kwamitin ta duba batutuwan mutanen da ake tsare da su wadanda kungiyoyin tallafawa al'umma da kungiyar lauyoyi na jihar Oyo suka gabatar don neman musu afuwa.

Ya ce abubuwa uku da ake dubawa wurin yin afuwar shine shekaru, rashin lafiya da tsawon zama a gidan gyaran hali kafin sakin wadanda suka amfana da afuwar.

Kotu ta daure manomi kan satar kwan kaji

A wani rahoton mai kama da wannan, kotu da ke zamanta a Epe a Legas ta daure wani Samuel Asam, dan shekara 31 a gidan yari kan satar kwan kaji.

An samu Asam da aikata laifuka biyu ne masu alaka da kutse cikin gida da sata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164