An garkame wani manomi a gidan yari saboda satar kwan kaji

An garkame wani manomi a gidan yari saboda satar kwan kaji

Kotun majistare da ke Epe a Legas ta yanke wa wani Samuel Asam mai shekaru 31 hukuncin zaman gidan yari na watanni biyu bayan an damke shi yana satar kaji da kwayayensu daga gidan gonan makwabcinsa.

Sai dai, Alkalin kotun, Mrs. F.O. Fowowe-Erusiafe ta bawa wanda aka yanke wa hukuncin zabin yin ayyukan taimakon al'umma na sa'o'i 40.

Kotun ta same Asam da ke zaune a kauyen Igbojia a Ibeju-Lekki da laifuka guda biyu wanda suka jibinci shiga gida ba tare da izini ba da kuma sata.

Shari'a sabanin hankali: Alkali ya tura wani da ya saci kwan kaji gidan kurkuku
Shari'a sabanin hankali: Alkali ya tura wani da ya saci kwan kaji gidan kurkuku

KU KARANTA: An kama sojan bogi dauke da katin shaidan jami'in 'dan sanda

Ana tuhumarsa da satan kaji da kwayayen kaji wanda kudinsu ya kai N527,600 daga gidan gonan makwabcinsa.

Wanda aka gurfanar gaban kotun ya amsa laifinsa, ya kuma nemi kotu tayi masa sasauci don a cewarsa bai san abinda ya tunkuda shi ya aikata laifin ba.

Dan sanda mai shigar da kara, Saja Moses Oyekanmi ya shaidawa kotu cewa a baya, wani Tosin Fadayemi da ke kauyen Igbojia ya shigar da karar cewa anyi masa satan kaji a ranar 2 ga watan Yuni.

Oyekanmi ya ce Asam ya sace kajin turawa Broilers guda 10 wanda kudinsu ya kai N420,000; Cockerels guda 17 wanda kudinsu ya kai N51,000; Zakaru 10 wanda kudinsu ya kai N17,500 da kuma krate din kwai 46 wanda kudinsu ya kai N39,100.

Ya ce Asam ya amsa cewa shine ya aikata satar amma hukumar yan sanda basu gano dukkan kayayakin da ya sace ba.

Mai shigar da karar ya ce laifin ya sabawa sashi na 287 da 308 (2) na dokar masu laifi na jihar Legas na shekarar 2015.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164