Hotunan 'Yan 7 da Lakcara a Anambra ta Haifa Sun Birge Jama'a

Hotunan 'Yan 7 da Lakcara a Anambra ta Haifa Sun Birge Jama'a

  • Wata Lakcara a jami'ar Nnamdi Azikiwe, Awka, babban birnin jihar Anambra fannin karatun kasuwanci ta haifi 'yan bakwai - 2 maza, 5 mata
  • Sai dai wani hanzari ba gudu ba, asibitin ya bukaci su biya N19 miliyan idan ba haka ba zasu daina kula da sauran jinjiraye 6, yayin da 1 ya rasu
  • N1.6 miliyan kadai iyayen suke da shi, yayin da mahaifiyar 'ya'yan ta bayyana yadda take aiki tun 2020 ba ko kwabo, iyayen sun yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su kawo musu daukin gaggawa

Anambra - Wata lakcara a sashin fannin kasuwanci (Business Administration) na Jami'ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK) babban birnin jihar Anambra ta haifi 'yan bakwai a ranar Lahadi.

An haifi jinjirayen - biyu maza da mata biyar a asibitin mata da yara na Obijackson a Okija cikin karamar hukumar Ihiala a ranar Lahadi, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ribas: ‘Yan Sanda Sun Damke Yaro Mai Shekaru 17 da Yayi wa Mata 10 Ciki

Lakcara ta haihu
Hotunan 'Yan 7 da Lakcara a Anambra ta Haifa Sun Birge Jama'a. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Sai dai, barin cikin ya gushe yayin da asibitin suke barazanar dakatar da basu kulawa ga sauran jinjiraye shidan idan iyayen suka gaza biyan N19 miliyan.

Sai dai, ba a biya mahaifiyarta albashinta ba tun lokacin da ta fara aiki a 2020, jaridar The Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mijin, Celestine Uzodike, wanda ya zanta da The Nation cikin kuka, ya ce farin cikin ya koma radadi saboda N1.6 miliyan kadai za su iya biya cikin N19 miliyan da asibitin ta bukata.

Yayi kira ga gwamnati, kungiyoyi da mutane masu hannu da shuni da su zo ga daukinsu saboda yanzu haka sun rasa daya daga cikin jinjiraye.

Uzodike dan asalin Omogho ne, cikin arewacin karamar hukumar Orumba, sannan karamin hadimi ne ga gwamna Chukwuma Soludo.

Ya koka game da yadda matarsa, duk da daukarta da aka yi aiki a matsayin lakcara, kwabo bai taba shigo mata a matsayin albashi ba, ko bayan mata karin girma zuwa lakcara 2.

Kara karanta wannan

Kungiyar Likitoci A Nigeria Na Shirin Shiga Yajin Aiki Sabida Kin Biya Musu Hakkokinsu Da Gwamnati Tayi

Mahaifiyar jinjirayen ta kara da cewa:

"Abun kawai nake bukata shi ne masu tallafi su zo garemu yadda za mu iya biyan N19 miliyan din da asibiti ke bin mu."

Manajan Asibitin, Chika Ndu-Okonkwo, ya bayyanawa The Nation yadda suka yi fari nciki da haihuwar, amma kudin da aka bukata N19 miliyan saboda kowanne jinjiri zai tsaya asibitin tsawon makonni shida zuwa takwas, wanda hakan zai ci kusan N3 miliyan duba da yadda a yanzu jinjirayen nauyinsu bai kai 1 kg ba kowannensu.

Mukaddashin kakakin UNIZIK, Mrs Chika Ene, ta ce bazata iya magana ba a inda take a lokacin. Kuma ba a samu ganawa da shugaban jami'ar ba shima.

'Yan sanda dun kama yaro mai shekaru 17 da ke aikin yi wa mata ciki a makyankyasar jarirai

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Ribas sun bayyana kama wani yaro mai shekaru 17 da yake wa mata ciki a makyankayasar jarirai.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban Kasa Mai 'Rowa' Najeriya Ke Buƙata, In Ji Peter Obi

An ceto matra kusan goma dauke da juna biyu tare da wasu da suka haihu wadanda ake biyansu N500,000 a karbe jariransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng