Kungiyar Likitocin Na Shirin Shiga Yajin Aikin Sai Mama ta Gani

Kungiyar Likitocin Na Shirin Shiga Yajin Aikin Sai Mama ta Gani

  • Ba kamar malaman jami'a ba, liktoci ba kasafai suka fiya tafiya yajin aiki ba, sai da suna yawan amfani da barazanar zuwan dan biya musu bukatu
  • Likitoci masu shirin kwarewa ne daga asibitoci da cibiyoyin lafiya a fadin Nigeria ke shirin shiga yajin aiki
  • Likitocin na taimakawa mutuka gaya musamman wajen duba marasa lafiya, duba da karancin manyan ko kuma wanda suka kware

Abuja - Kungiyar likitoci masu shirin kwarewa NARD, tayi gargadin shiga yajin aiki in gwamnati ta gaza biya mata bukatunta.

Kungiyar a cikin wasikar da ta aikewa ministan lafiya na tarayya Nigeria, Osagie Ehanire a ranar Litinin dinnan wadda shugaban kungiyar ya sawa hannu, tace zata fara yajin aikin ranar 24 ga watan janairun wannan shekarar.

Wadannan likitocin dai na neman kwarewa ne a fannoni da dama na bangaren likitanci, wanda bayan kwarewar tasu suke zama manayn likitoci. Rahotan Premium Times

Kara karanta wannan

Bidiyon Zabgegiyar Damisa Tana Takun Isa Cikin Jama'a Da ke Shakatawa ya Janyo Cece-kuce

Lafiya
Kungiyar Likitocin Na Shirin Shiga Yajin Aikin Sai Mama ta Gani Hoto: UCG
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

kamar wata shida da suka shude, kungiyar ta bayar da wa'adin ga gwamnati kan ta biya wa 'ya 'yanta abubuwan da suke ci musu tuwo a kwarya da kuma duba ko gyara kudin asusun hadaka na lafiya wanda ake kira da MRTF.

Me yasa zasu tafi yajin aikin?

Likitocin na bukatar a zatar da dakar biyan kudinsu na aiyukan hatsari da suke yi nan take da kuma wasu ariyas - ariyas da suke bi.

Kungiyar tace akwai ariyas-ariyas na shekarun 2014 dana 2015, 2016 da ba'a biya su ba duk da zama da kuma tattaunawa da suke yi da gwamnati.

Sannan kungiyar tace bama a batun kaddamar da mafi kankantar albashi da ga 'ya 'yanta da kuma rashin biyansu wasu hakokin da suka cancanta a biya su, baya ga kin sanya su a tsarin biyan albashin tsarin lafiya na likitanci.

Kara karanta wannan

Ana bata sunan shugabanmu: Hukumar DSS ta fusata kan yadda ake cece-kuce game da Yusuf Bichi

Lafiya
Kungiyar Likitocin Na Shirin Shiga Yajin Aikin Sai Mama ta Gani Hoto: UCG
Asali: UGC

Likitocin sun ce duk da an biya wasu daga cikin bukatun nasu amma akwai da yawa daga cikin bukatun nasu da ba'a biya ba, wanda sune ma suka fi yawa kuma sune dalilin da yasa zasu tafi yajin aikin.

"Mun yaba da kudirin gwamnati na biya mana wasu daga cikin bukatun mu ta hannun ma'aikatar lafiya da hukumomin gwamnati
"Duk da haka akwai bukatun mu masu tarin yawa da ba ma a bi ta kansu ba, wanda sune kanwa uwar gamin ko dalilin da yasa zamu tafi yajin aikin." inji sanarwar

Yajin aikin

Jaridar vanguard ta rawaito cewa kungiya na shirin fara yajin aikin nata ne muddin gwamnati bata biya mata bukatunta ba.

Ta ce babu abinda zai hana ta tafi yajin aikin inda abinda suka fada bai yiwu ba.

Gwamnati da kungiyar likitoci masu shirin kwarewa NARD

A Nuwanban shekarar bara ne dai gwamnati ta sanar da tsarinta na gayara tare da duba albashin likitoci da ma'aikatan lafiya dan magance barazanar yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel