Kotu Ta Soke Dokar da Ta Hana Jami’an ’Yan Sanda Mata Marasa Aure Yin Ciki
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kori wata daga cikin jami'anta bisa laifin yin ba tare da aure ba
- An ruwaito cewa, rundunar na da dokar da ta haramtawa jami'ai mata yin ba tare da aure ba a lokacin da suke aiki
- Wata kotu ta soke dokar tare da bayyana hujjojin cewa, dokar ta nuna wariya ga mata jami'ai marasa aure
Akure, Ondo - Kotun masana'atu ta soke dokar da rundunar 'yan sandan Najeriya ta saka na kange jami'anta mata daga yin ciki ba tare da aure ba, TheCable ta ruwaito.
A ka'idar da rundunar ta kawo na aiki a sakin layi na 127, duk wata jami'ar da ta dauki ciki ba tare da aure ba za a kore ta a aiki.
A baya kunji wani rahoton da yake cewa, wata mata a rundunar 'yan sandan Najeriya, Omolola Olajide ta yi, wannan yasa aka kore ta a aiki a shekarar 2021.
Kwamishinan 'yan sanda, Babatunde Mobaya ya ce an kori wannan jami'ar ne daidai a tanadin dokar 'yan sanda sashe na 127.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Batu ya tafi kotu
Bayan korarta, kwamishinan shari'a na jihar Ekiti, Olawale Fapohunda ya kai batun gaban kotu tare da neman babbar kotun tarayya da ke zama a Ekiti ta soke dokar 'yan sanda sashe na 127.
Sai dai, kotun a kori karar tare da cewa hakan ya saba doka, domin kuwa Olajide tuni ta kai batun gaban kotun masana'antu na Najeriya.
Hukuncin da aka yanke
Da yake yanke hukunci a kotun kan kara mai lamba NICN/AK/14/2021, mai shari'a Dashe Damulak na kotun masana'antu a birnin Akure ya ce sashen dokar 'yan sandan ya tauye hakkin wasu jami'ai, don haka ya soke shi.
Duk da cewa an yanke hukuncin soke dokar, amma mai shari'a ya ce ba za a maida Olajide aikin 'ya sanda ba, rahoton Premium Times.
Ya yanke ba za a maida ita bane saboda a cewarsa, lokacin da aka kore ba tabbatar da ita a matsayin cikakkiyar ma'aikaciya ba
Sai dai, ya umarci rundunar da ta ba Olajide N5m a matsayin diyyar take hakkinta da kuma nuna mata wariya.
A tun farko an kama jami'ar ne a shekarar 2021, inda aka dakatar da ita bisa laifin yin ciki ba tare da aure ba.
Asali: Legit.ng