Yan Bindiga Sun Halaka Yan Bijilante 3 A Wata Jihar Najeriya

Yan Bindiga Sun Halaka Yan Bijilante 3 A Wata Jihar Najeriya

  • Wasu yan bindiga sun kai hari a sakatariyar karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra sun kona gine-gine tare da halaka yan bijilante uku
  • Kakakin yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da afkuwar harin ya kuma ce an tura jami'ai yankin don tabbatar da tsaro
  • Ikenga ya ce jami'an tsaron da suka amsa kirar neman daukin sun halaka daya cikin yan bindigan kuma sun kwato makamai daban-daban

Jihar Anambra - Yan bindiga sun kai hari sun kashe yan bijilante guda uku a jihar Anambra, sun kuma cinnawa gidaje biyar wuta.

The Punch ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ihiala da ke jihar ta Anambra misalin karfe 2 na daren Alhamis.

Wata majiya daga yankin ta ce bayan harin da kashe yan bijilanten uku a sakatariyar karamar hukumar, sun datse kan daya cikinsu.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kashe Shugaban Kungiyar Fityanul Islam Da Dan Uwansa, Sun Sace Matan Aure 4 A Kaduna

Gini a Anambra
Yan Bindiga Sun Halaka Yan Bijilante 3 A Wata Jihar Najeriya. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Ya ce yan bindigan sun kuma yi amfani da abin fashewa sun kona gidaje biyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani rahoto da ba a tabbatar ba ya ce daya daga cikin gidajen gini ne na hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC.

Jami'an tsaro sun kai dauki, sun hallaka dan bindiga daya, Kakakin Yan sanda

A yanzu ba a tabbatar da dalilin kai harin ba amma kakakin yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da lamarin.

Ikenga ya ce an sanar da yan sanda kuma lokacin da suka isa wurin, yan sandan sun kashe daya cikin yan bindigan bayan musayar wuta.

Ya tabbatar da cewa a lokacin da yan sandan suka amsa kiran neman daukin, yan bindigan sun kashe yan bijilante uku da ke aiki, sun kona gidaje biyar, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Abin kunya: Bidiyon yadda kyamara ta dauki 'yan sanda na yunkurin yin fashi da makami

Ya ce yan sanda da sojoji suna nan a yankin a halin yanzu.

Ya ce:

"Biyo bayan atisayen yan sanda/sojoji a Ihiala da garin da ke makwabtaka da shi, jami'an tsaro sun amsa kirar neman dauki misalin 2.55am, yau 12/1/2023 kan harin da aka kai karamar hukumar Ihiala.
"Yan sandan sun kashe daya cikin maharan, sun kwato abin na'urar harba abin fashewa biyu, abin fashewa bakwai, harsashin AK47 mai tsawon 7.62MM, wukake, layyu, da wasu makamai masu hatsari.
"Maharan sun riga sun halaka yan bijilante uku da ke bakin aiki, sun datse kan daya sun kona gidaje biyar da bam na fetur.
"Jami'an tsaron sun fafata da maharan, sun hana su cigaba da barnar yayin da wasun sun sun tsere da rauni.
"An dauko gawarwarkin wadanda abin ya faru da su kuma ana cigaba da atisayen. Za a bada karin bayani nan gaba."

Mahara sun kai hari ofishin INEC a jihar Imo

Kara karanta wannan

Bidiyon Zabgegiyar Damisa Tana Takun Isa Cikin Jama'a Da ke Shakatawa ya Janyo Cece-kuce

A wani rahoto, mahara da sanyin safiyar Litinin 12 ga watan Disamba sun kai hari ofishin INEC da ke Owerri, jihar Imo.

The Punch ta rahoto cewa sun lalata wasni sashi na ginin ofishin sakamakon bam da suka dasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164