Za Ku Iya Biyan JAMB Ta Hanyar Amfani da eNaira, Rahoto Ya Bayyana Ta Yaya
- Hukumar jarrabawa ta JAMB ta ce, za a iya biyan kudin jarrabawar UTME ta hanyar amfani da eNaira
- Masu son rubuta JAMB za su sauke manhajar eNaira, su daura ta a waya domin siyan fom da cike shi cikin sauki
- Babban bankin Najeriya (CBN) da JAMB ne suka hada kai don tabbatar da an saukakewa 'yan Najeriya wahala
Najeriya - Hukumar shirya jarrabar shiga manyan makarantun gaba da sakadanre (JAMB) ta ce za ta hada kai da CBN don tabbatar da karbar kudi ta hanyar amfani da kudin eNaira.
CBN ta ce yin hakan zai taimaka wajen rage wahala ga daliban da ke son yankan fom din rubuta jarrabarar a Najeriya.
Wannan na fitowa ne daga bakin daraktar IT da dabaru na CBN, Rakiya Mohammed yayin da take tattaunawa da masu ruwa da tsaki na bankin kasar.
Dalilin kawo wannan dabarar
Rakiya dai ta samu wakilcin Abdul Shedrack ne a wannan taron da aka gudanar mai dimbin tarihi ga masu rubuta JAMB, The Times ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rakiya ta bayyana cewa, hadin gwiwar JAMB da CBN zai rage cutar dalibai da ake wajen biyan kudin jarrabar a cibiyoyin rajista a fadin kasar.
A cewarta, unkurin zai habaka aniyar amfani da fasahar zamani wajen rage yaduwar kudade da gwamnatin Najeriya ta dauko kwanan nan.
Ta kuma jaddada cewa, eNaira dinnan ba komai bane face adadi da darajar kudi Naira amma a bisa tsari na fasaha.
Saboda haka, Rakiya ta ce, amfani da eNaira akwai sauki, kuma bai da wata matsala da za ta kawo cikas ga batan kudi.
Yadda za a yi amfani da eNaira wajen biyan JAMB
CBN ya bayyana cewa, duk mai son amfani da eNaira wajen biyan JAMB, zai iya sauke eWallet a manhajar Google Play Store kuma Apple Store.
A wani rahoto, an gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya ce an yi amfani da manhajar akalla sau 700,000, ta yu hada-hadar kusan N8bn kenan daga ranar da aka kaddamar da ita a ranar 25 ga watan Oktaban 2021.
An kirkiri wannan manhaja ne dai don rage amfani da tsabar kudi a hannu, lamarin da gwamnatin Najeriya ke ci gaba da daukar dumi a kai.
A tun farko an fitar da jadawalin jarrabawar JAMB ta shekarar 2023, ana ci gaba da kai ruwa rana a jami'o'in Najeriya.
Asali: Legit.ng