Abun Bakin Ciki Yayin da Yan Bindiga Suka Kashe Amarya da Ango Yan Kwanaki Kafin Bikinsu

Abun Bakin Ciki Yayin da Yan Bindiga Suka Kashe Amarya da Ango Yan Kwanaki Kafin Bikinsu

  • Jahar Imo da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya na fama da hare-haren yan bindiga a na tsawon lokaci yanzu
  • Wani harin baya-bayan nan da ya afku shine na kisan wasu masoya yan kwanaki kafin shagalin bikinsu

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wasu ma’aurata da ke hanyarsu ta komawa mahaifarsu don bikin aurensu a jihar Imo.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa an kasha ma’auratan masu suna Ezemezie Ifechukwu Martins da Mba Ifeoma Gloria a daren ranar Talata, 10 ga watan Janairu a Ndiejezie Izuogu, karamar hukumar Ideato ta arewa da ke jihar.

Jami'an yan sanda
Abun Bakin Ciki Yayin da Yan Bindiga Suka Kashe Amarya da Ango Yan Kwanaki Kafin Bikinsu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Abun da ya faru

A cewar wata majiya a yankin, an kasha masoyan ne yan kwanaki kafin daurin aurensu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kashe Shugaban Kungiyar Fityanul Islam Da Dan Uwansa, Sun Sace Matan Aure 4 A Kaduna

An kuma tattaro cewa kanin angon ma ya rasa ransa a yayin harin.

Yadda aka kashe masoyan, majiya ta bayyana

Majiyar wacce ta zanta da jaridar TheCable ta ce maharan sun kasance kasurguman masu kwacen mota ne a yankin, yana mai cewa suna kashe masu ababen hawar da suka ki mika wuya.

“Yanzu ba mu tsira ba a Arondizogu. Dalibai na tsoron zuwa makaranta. Iyayenmu mata sun daina zuwa kasuwa saboda tsoron abun da ka iya faruwa," cewar majiyar.

Mazauna sun tsere daga garin

“Yanzu haka da muke Magana, mutane masu yawan gaske sun bar Arondizogu a safiyar nan bayan afkuwar lamarin na daren jiya.
“Na yi korafin wannan sace-sace da kashe-kashen mutane da kona-konen motoci a Arondizogu a bara, kuma kakakin yan sandan jihar Imo ya bani tabbacin cewa an rigada an dauki mataki a kai.
“Amma tun bayan nan, kashe-kashe da sace-sacen mutane ya zama ruwan dare.
“Mutanenmu da ke turai sun ki dawowa bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara. Yan kadan da suka dawo basu iya yawo da motocinsu ba. Wannan abun bakin ciki ne.

Kara karanta wannan

Kaico: 'Yan bindiga sun kashe mutane da yawa a wata jiha, har da mata mai juna biyu

“Muna kira ga gwamnatin jihar Imo da ta kawo mana agaji sannan ta turo sojoji don su karbe yankin da nufin kawo karshen kashe-kashen,” cewar majiyar.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Michael Abattam wanda ya tabbatar da lamarin ya kara da cewar ba shi da tabbacin mutuwar amaryar. rahoton The Sun.

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta koka kan yadda yar aikin gidansu ta zuba mata guba a cikin man shafarta wanda ya yi sanadiyar illata mata fuska.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng