Kwamandojin ISWAP 10 da Suka Arce Daga Harin Boko Haram Sun Mika Wuya ga Hukumomi

Kwamandojin ISWAP 10 da Suka Arce Daga Harin Boko Haram Sun Mika Wuya ga Hukumomi

  • Labarai da ke zuwa masu dumi shi ne na tuban manyan kwamandojin ISWAP 10 da 'yan ta'addan Boko Haram suka kaiwa hari a cikin makon nan
  • An gano cewa, kwamandojin karkashin jagorancin Abou Moussab Al-Barnawiy sun tsere zuwa Nijar inda suka mika wuya ga hukumomi
  • Yaki tsakanin kungiyoyin ta'addancin biyu ya ki ci balle cinyewa inda masana ke ganin hakan kila ya zamo silar tarwatsewar ta'addanci a arewa maso gabashin Najeriya

Mayakan ta'addancin ISWAP 10 da suka tsere daga harin takwarorinsu na Boko Haram a Kayowa da Toumbun Gini a raewa maso gabashin tafkin Chadi sun mika wuya ga hukumomi a jamhuriyar Nijar.

Borno map
Kwamandojin ISWAP 10 da Suka Arce Daga Harin Boko Haram Sun Mika Wuya ga Hukumomi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Majiyoyin sirri sun sanar da Zagazola Makama cewa mayakan ISWAP din sun mika wuya ga hukumomin a ranar 10 ga watan Janairun 2022 duk a cikin tsoron rasa ransu sakamakon artabun da suke da abokan hamayyarsu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-duminsa: Hoton Atiku Cikin Murmushi Ya Bayyana Yayin da Ake Rade-radin Bai Da Lafiya

Farmakin da Boko Haram ta kai wa ISWAP din sansanoninsu ya yi sanadin mutuwar mayakansu masu tarin yawa tun daga ranar 31 ga watan Disamba har zuwa 8 ga Janairun 2023.

Cigaba da kai farmakin da Boko Haram ke yi karkashin jagorancin kwamandansu Abu Umaimah wanda aka fi sani da Baoura Doro, yayi sanadin lalacewar sansanonin 'yan ta'addan da ke Toumbum Allura, Kurnawa, Kayowa da Toumbun Gini, lamarin da yasa Abu Moussab al-Barnawi da sauran kwamandojin arcewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Cigaban fada tsakanin kungiyoyin ta'addancin biyu masu hamayya da juna kamar ya ki zuwa karshe saboda kokarinsu na hada kai da rundunar sojin Najeriya da na farar hula ya ci tura.

A saboda hakan ne ISWAP ido rufe suke neman goyon bayan ISIS daga Mali, Burkina Faso da Somalia don su taimaka musu wurin ganin bayan JAS.

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

Zagazola Makama ya gano cewa, Albarnawwy ya dawo tafkin Chadi a ranar 10 ga watan janairu tare da mayaka 300 don su kaddamar da mummunar hari kan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram.

Yayin da wannan hargitsin ka iya zama alheri ga dakarun sojin Najeriya, Operation Hadin Kai na iya amfani da damar wurin ragargaza 'yan ta'addan tare da kawo karshen ta'addanci a yankin baki daya.

'Yan bindiga sun kai farmaki Birnin Gwari, sun halaka jami'an tsaro

A wani labari na daban, miyagun 'yan bindiga a jihar Kaduna sun kai hari yankunan karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

An gano cewa, sun harzuka da halaka musu yaron da le musu kiwon shanun sata, hakan yasa suka sauke fushinsu kan jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng