Kotun Najeriya Ta Yanke Wa Wasu Ƴan Fashi Ɗaurin Shekara 56 A Gidan Yari
- Kotu ta yi wa wasu maza biyu daurin shekara 56 a gidan gyaran hali a, Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom
- Hakan ya faru ne bayan kotun ta same su da laifin hadin baki tare da yi wa wani fashin kwamfutansa da wayar salula
- Mutum na uku cikin wadanda ake zargin shi kuma kotun ta wanke shi sannan ta sallame shi saboda rashin hujjar cewa ya aikata laifi
Akwa Ibom - Wata babban kotu da ke zamanta a jihar Akwa Ibom, ta yanke was wasu mutane biyu da aka samu da laifi daurin shekaru 28 a gidan yari kan yi wa wani fasinja da ke kokarin hawa adaidaita fashi a Okokon Etuk Street, Uyo, babban birnin jihar.
Mai shari'a Okon Okon ne ya yanke wa wadanda aka samu da laifin, Nsikan Tom, wanda aka fi sani da 'Nokia' dan shekara 28, da Agustine Gregory, dan shekara 27 a ranar Talata, The Punch ta rahoto.
Amma kotun ta wanke mutum na ukun da ake zargi, Daniel Okon, daga dukkan laifukan uku na hadin baki, fashi da makami da zama mamban haramtacciyar kungiya.
Mai shari'a Okon, yayin hukuncin da aka shafe kimanin awa ɗaya da minti 30, ya ce kotun ta samu sauran wadanda ake zargi biyun da aikata laifin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Don haka ya yanke musu daurin shekara 21, kan laifin fashi sai shekara bakwai kan laifin hadin baki, ya ce a gwamutsa musu shekarun tare.
Masu shigar da kara sun gamsar da kotu cewa an aikata fashi, in ji Kotu
Kotun ta ce duk da cewa masu shigar da kara ba su gamsar da kotu cewa an yi amfani da bindiga ba, akwai isasshen hujja da ke nuna an yi wa wanda abin ya faru da shi fashin kwamfutansa Lenovo da wayarsa Gionee M5 a ranar 7 ga watan Agustan 2016.
Alkalin ya wanke wadanda ake zargin kan zama mambobin kungiyar asiri, yana mai cewa "babu dokar da ta haramta yi wa yan sanda bayani."
Kotun ta yi bayanin cewa "masu shigar da karar na neman a hukunta wadanda aka yi kara saboda sun fada wa yan sanda a hedkwata da ke Ikot Akpan, Abia, cewa su mambobin wata haramtacciyar kungiya ne."
Yan uwan wadanda aka yanke wa hukuncin sun rika sharbar kuka a harabar kotun bayan yanke hukuncin.
Kotu ta daure wani da aka kama da katin zabe 101
A wani rahoton, kotu ta yanke wa wani mutum da aka kama da katin zabe guda 101 hukuncin daurin shekara daya a gidan yari a cewar hukumar INEC.
Kamar yadda The Cable ta rahoto, INEC ta ce an hukunta mutumin ne cikin wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai na hukumar, Festus Okoye ya fitar.
Asali: Legit.ng