Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Kasuwa a Jihar Neja Suka Ki Karbar Sabbin Kudin da Aka Fitar

Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Kasuwa a Jihar Neja Suka Ki Karbar Sabbin Kudin da Aka Fitar

  • Yayin da ake ci gaba da sanya ido kan cikar wa'adin lokacin da CBN ta diba na kawo karshen kashe tsoffin kudi, mutane sun ki sabbin Naira
  • A halin da ake ciki, mutanen karkara a jihar Neja sun ki karbar sabon kudi, 'yan kasuwa suna ci gaba da fuskantar matsala
  • CBN ta ce tana ci gaba da wayar da kan jama'a, har yanzu mutane basu gama gamsuwa da sabbin Naira ba

Jihar Neja - Kwanaki kadan gabanin cikar wa'adin da CBN ta sanyawa wasu daga tsofaffin kudin Najeriya, 'yan a kasar basu gama gamsuwa da fara karba ko kashe sabbin kudi ba.

Wannan lamari dai ya fi yawa a karkara, inda wasu sam basu ma san da batun sauyi ba, wasu kuwa sun sani amma zukatansu basu aminta ba, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga karshe, shakku ya kare kamfanin da ya buga sabbin Naira ya yi bayanin kankat

Ga wadanda suka san da kudin sun fara yawo, suna ganin kamar 31 ga watan Janairu ba zai zama gaskiya ba ace lokacin wa'adin karshe na tattara tsofaffin kudaden kasar.

Sabbin Naira na Buhari: 'Yan Neja suna ci gaba da kin karbar sabbin kudi
Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Kasuwa a Jihar Neja Suka Ki Karbar Sabbin Kudin da Aka Fitar | Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A cewar wasu, tabbas za su nemi karin wa'adin a wurin gwamnati domin tabbatar kwashe gaba dayan kudaden zuwa bankunan kasar,

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai, babban bankin Najeriya (CBN) na ci gaba da bayyana matsayarsa cewa, ba zai kara wa'adi kan 31 ga watan Janairu ba.

Ana wayar da kan mutane game da sabbin Naira

CBN reshen jihar Neja karkashin kwanturola Ademola Mohammed Saheed tuni ya fara gangamin wayarwa mutane kai game da dawo da tsoffin kudi da kuma fara amfani sabbin da aka fitar; musamman ga 'yan kasuwa a kauyuka, rahoton The Nation.

A cewar 'yan kasuwa a jihar, akwai matukar wahala yin harkallar kasuwanci tsakanin mutanen karkara saboda har yanzu sukan ki karbar sabbin kudin a hannun mutane.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Wani Mai Hannu a Garkuwa Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya, Ya Fara Bayani

Hakazalika, sun ce bankuna da injunan ATM a fadin jihar na ci gaba da ba tsoffin kudi, wanda hakan ne babban makasudin ci gaba da yaduwar tsoffin kudi a tsakanin 'yan kasuwa.

Abin da 'yan kasuwa ke cewa

Daya daga cikin 'yan kasuwan da aka zanta dasu, Yusuf Mohammed ya bayyana cewa:

"Mutanen da ke rayuwa a karkara masu da batun sabbin Naira ba da wa'adinsa kuma basa ma karbar sabbin kudin daga wadanda suka samu damar samu.
"Ina ganin akwai bukatar fadada wayar da kai game da sabbn kudin don fahimtar da su cewa kudi ne na gaske."

Shugabar mata 'yan kasuwa a jihar, Rebecca James ta bayyana koken cewa, 'yan kasuwa na kin karbar kudaden a lokacin da aka siya kayayyakinsu.

Ta kuma bayyana cewa, hakan tabbas na shafan tafiyar da kasuwancinsu da kuma harkokin da suke na yau da kullum.

A ranar 31 ga watan Janairun nan ne za a daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1,000 a Najeriya.

Kara karanta wannan

Akwai Isassun Sabbin Kudi A Bankuna, Bamu Hana Badasu a Kanta Ba: CBN Tayi Martani

Dokar kayyade kuwa, ta fara aiki ne daga ranar Litinin din da ta gabata, 9 ga watan Janairu, kamar yadda aka tattaro a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.