Ba Zan Tursasa Zabin Dan Takararar Shugaban Kasa Na a Benue, Gwamna Ortom Ya Magantu

Ba Zan Tursasa Zabin Dan Takararar Shugaban Kasa Na a Benue, Gwamna Ortom Ya Magantu

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya ce har yanzu bai bayyana dan takarars hugaban kasan da yake goyon baya ba a zaben bana mai zuwa
  • Ortom ya karyata labarin cewa ya bayyana wanda yake goyon baya a ranar Talata 10 ga watan Janairu
  • Gwamnan na Benue ya ce, rahoton da ke cewa yana goyon bayan Atiku Abubakar na jam'iyyarsu ta PDP karyace, kuma hakan ya saba da aniyarsu ta gwamnonin G-5

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya yi martani ga rahoton da ke cewa yana goyon bayan Atiku Abubakar a zaben 2023 mai zuwa nan da wata guda.

Ortom ya karyata yana goyon bayan Atiku ABubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, wanda shine dan takarar jam'iyyar su Ortom.

Gwamnan na Benue ya bayyana cewa, bai bayyana wanda yake goyon baya ba, kuma ba zai tursasawa mutanensa bin wani dan takara ba, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamnonin G5 Sun Goyi Bayan Atiku A Sirrance? Sabbin Bayanai Sun Bayyana

Ortom ya magantu game da matsayarsa ta goyon bayan Atiku
Ba Zan Tursasa Zabin Dan Takararar Shugaban Kasa Na a Benue, Gwamna Ortom Ya Magantu | Hoto: dailyppost.com
Asali: UGC

Ba zan tursasawa kowa bin zabi na, inji gwamna Ortom

Terver Akase, hadimin Ortom a fannin yada labarai ya fitar da wata sanarwar da ke cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar sanarwar:

“Lokacin da gwamna ya gana da jiga-jigan jam’iyyar PDP a jiya, 9 ga watan Janairu, 2023, a gidan gwamnatin jihar Benue da ke Makurdi, sakon da ya aike musu a bayyane yake karara cewa shugabannin jam’iyyar PDP na kasa sun gaza magance rikice-rikicen cikin gida da suka haifar da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.
"Gwamna ya fadi a lokacin ganawar cewa idan ba a warware rikicin ba kafin zabe, bai da zabin da ya wuce ya dauki mataki game da lamarin. Ya kara da cewa, duk da haka, cewa ba zai tursasa zabinsa ga mambobin jam'iyyar a jihar ba."

Babu ruwa na da Atiku, inji Ortom

Kara karanta wannan

2023: A Karshe, Atiku, PDP Sun Samu Sako Mai Karfafa Zuciya Daga Gwamnonin G5

Da yake martani game da jita-jitan cewa yana goyon bayan Atiku, sanarwar da aka fitar ya ce gwamnan ya bayyana karara cewa karya aka yada a kansa.

Hakazalika, ya ce idan har ya goyi bayan Atiku, to ya saba amintar da ke tsakaninsa da gwamnonin G-5 masu adawa da gwamnatin jam'iyyar, rahoton TheCable.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Makirkira wannan rahoton tabbas a matse suke su cimma wata manufa mai araha ta tsinin siyasa."

Gwamnonin G-5 dai na ci gaba da bayyana adawa da Atiku da kuma shugabancin PDP, a kwanakin baya aka zargi suna kokarin marawa Tinubu baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.