Jama'a Dauke da Makamai Sun Budewa Jami'an NDLEA Wuta a Legas

Jama'a Dauke da Makamai Sun Budewa Jami'an NDLEA Wuta a Legas

Legas - Wasu jama'a dauke da makamai a daren Litinin sun budewa jami'an Hukumar Yaki da Fasa-kwabrin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, wuta a kan titin Awolowo duk a kokarinsa na hana jami'an kama wani direban babbar mota da ya dankaro ta da buhunan wiwi.

Labari
Jama'a Dauke da Makamai Sun Budewa Jami'an NDLEA Wuta a Legas
Asali: Original

Wata majiya ta sanar da Vanguard cewa, jama'ar masu dauke da bindigu ana zargin jami'an wata hukumar tsaro ne kuma sun ragargaza daya daga cikin ababen hawan hukumar NDLEA din.

Sai dai, taimakon wasu sojoji ne ya hana abinda ka iya haifar da kare jini, biri jini a titin, lamarin da yasa bata-garin suka arce har da direban inda suka bar babbar motar.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel