Mun Sha Wahala Sosai, Kada Ku Bari Wani Ya Sake Wargaza Mu, Buhari Ga ’Yan Najeriya

Mun Sha Wahala Sosai, Kada Ku Bari Wani Ya Sake Wargaza Mu, Buhari Ga ’Yan Najeriya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce akwai wadanda burinsu kawai su ga an wargaza Najeriya
  • Buhari ya ce akwai bukatar ‘yan kasar nan su maida hankali tare da samun kwarin gwiwa game da Najeriya
  • Saura watanni hudu suka rage shugaban ya sauka, ya ce zai ci gaba da aikin inganta tsaron kasar

Damaturu, jihar Yobe - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, akwai bukatar ‘yan Najeriya su gina kwarin gwiwa mai karfi game da kasar nan.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a fadar sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi a ziyararsa ta jihar Yobe, TheCable ta ruwaito.

A cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina a fitar, Buhari ya ce akwai bukatar ‘yan Najeriya su kauracewa ayyukan da ka iya kawo cikas ga tsaron kasar.

Kara karanta wannan

2023: Abinda Shugaba Buhari Ya Fada Wa Mutanen Adamawa Game da Zaben Mace Ta Zama Gwamna

Buhari ya magantu game da halin da kasar nan ke ciki
Mun Sha Wahala Sosai, Kada Ku Bari Wani Ya Sake Wargaza Mu, Buhari Ga ’Yan Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban ya kuma bayyana cewa, duk da saura masa watanni kadan ya sauka a mulki, amma zai ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da ci gaban tsaron kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abin da Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya su maida hankali a kai

A cewar sanarwar:

“Da watanni hudu da nake dashi a matsayin shugaban kasa, zan ci gaba da jajircewa kuma ina fatan yin ritaya a cikin aminci.
“Dole ne mu gina kwarin gwiwa mai karfi game da kasarmu. Ya kamata mu zama ba ma kawo cikas ga lamarin tsaro ta kowacce hanya saboda tsaro da tattalin arziki su ne abubuwa mafi muhimmanci.
“Mun sha wahala sosai yawa a matsayinmu na kasa kuma ina kira gareku da ku kasance masu jajircewa kuma ku tabbatar bamu bari wani ya sake wargaza mu ba.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban Kasa Ya Tsira Daga Yunkurin Tsige Shi a Majalisar Dattawa – Sanatan PDP

“Akwai wadanda da gangan ke son ganin sun wargaza Najeriya amma Allah ba zai barsu ba, Allah ya taimaki Najeriya ta farfado.”

Mun kubutar da Yobe daga mamayar 'yan ta'adda, inji gwamna Buni

Da yake magana a wurin taron, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya shaidawa Buhari cewa, a lokacin da 'yan ta'adda ke kan ganiyar barna a Yobe, fadar Damaturu sai da ta koma karkashin hannun 'yan ta'adda.

Sai dai, ya ce a yanzu an samu nasara, domin an fatattaki 'yan ta'adda, kuma ana ci gaba da samun nasara a kansu, rahoton This Day.

A kalamansa:

"Saidai, a yau abin dubawa ne cewa jihar Yobe na daga cikin jihohin da ka 'yanta daga mamayar 'yan ta'addan Boko Haram."

Duk da yadda aka yaba Buhari, wani jigon siyasa a Najeriya yi masa kudin goro da dukkan 'yan APC, ya ce kanwar ja ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.