Gwamnatin Buhari Ta Fadawa Kamfanin NNPC Ya Rage Farashin Fetur a Najeriya

Gwamnatin Buhari Ta Fadawa Kamfanin NNPC Ya Rage Farashin Fetur a Najeriya

  • A maimakon a samu riba a wajen saida man fetur, gwamnatin tarayya ta ce asara NNPC take yi a Najeriya
  • Timipre Sylva ya ce an ba kamfanin NNPC umarni ya rika saida fetur da araha domin gudun farashi ya tashi
  • Karamin Ministan harkokin man fetur ya nuna ba za ta yiwu gwamnati ta cigaba da biyan tallafin fetur ba

Abuja – An samu labari kamfanin mai na kasa wanda aka fi sani da NNPC, yana tafka asara ne a wajen saida man fetur saboda nauyin da yake kan sa.

A ranar Litinin, 9 ga watan Junairu 2022, Punch ta rahoto karamin Ministan harkokin fetur na kasa, Timipre Sylva yana bayanin halin da ake ciki.

Cif Timipre Sylva ya yi magana ne sa’ilin da aka cigaba da taron da ake yi domin a zayyano irin nasarorin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu.

Kara karanta wannan

Boka Ya Yi Mummunan Karshe, Ya Mutu a Wajen Lalata da Uwargidar Wani Fasto

Ministan harkokin man ya sake jaddada cewa tallafin man fetur da ake biya ya zama ala-ka-kai ga gwamnati a lokacin da ake neman kudin da za ayi ayyuka.

Ana kona kudi a iska kurum - Minista

Mutane su na kona wadannan kudi da ake batarwa ne a cikin motocinsu kurum.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon Gwamnan na Bayelsa yake cewa yana mamakin yadda ake cigaba da rike kasar nan a haka domin asara gwamnati take yi a wajen saida mai.

Man fetur
Gidan man fetur a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Mai girma Ministan yana bada misali da cewa tamkar mutum ya saye kaya ne a kan N10, amma idan ya tashi saidawa sai ya karbi abin da bai kai hakan ba.

A kullum kenan mutum zai rika neman karin kudin da zai saye wannan kaya domin bai samun riba. A irin haka ne tsarin biyan tallafin man fetur ya daure.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Wani matashi ya yi tsaurin ido, ya sace mahaifinsa, an ba kudin fansa N2.5m

An rahoto Ministan tarayyar yana cewa daukar dawainiyar rike farashin man fetur saboda tsoron a tsawwala, ba abu ne mai sauki a wajen gwamnati ba.

Mai zai iya komawa N300?

Da aka yi masa tambaya a game da sayen litar man fetur a N300, karamin Ministan ya ce ba zai ji babu dadi ba, domin haka farashin yake a sauran kasashe.

A cewarsa, abin takaicin shi ne har gobe gwamnati ta na biyan tallafin da ba zai yiwu a cigaba da shi ba, Sylva ya nuna nan gaba fetur zai kara tsada a Najeriya.

A game da gyaran matatun danyen man da ke kasar, tsohon Gwamnan na Bayelsa ya ce a farkon shekarar nan matatar Fatakwal za ta fara tace ganguna 60, 000.

EFCC ta gano cuwa-cuwa

Rahoto ya zo a baya cewa binciken da Jami’an EFCC suka gudanar ya nuna daga 2017 zuwa 2021, N12,998,963,178.29 aka biya barayi da nufin tallafin man fetur.

Badakalar ta fara ne daga wajen hako danyen mai zuwa shigo da man da aka tace, sannan wasu su kan karkatar da fetur daga gidajen mai zuwa kasar waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng