Wata Mata Ta Ba da Mamaki Yayin da Ta Ce Tana da Shekaru 28, Amma Ta Haifi ’Ya’ya 9

Wata Mata Ta Ba da Mamaki Yayin da Ta Ce Tana da Shekaru 28, Amma Ta Haifi ’Ya’ya 9

  • Wata mata ta bayyana haihuwar yara tara duk da kananan shekaru da take dashi, ta yada bidiyon ‘ya’yanta gaba dayansu
  • Kyakkyawar matar mai kuruciya da yawa a jiki ta yada hotunanta da dukkan ‘ya’yanta, inda tace daya daga cikinsu ya mutu
  • Jama’ar kafar sada zumunta sun yi mamakin sirrinta na kasancewa da kwari duk da haihuwar yara masu yawan gaske

Wata uwar ‘ya’ya da yawa mai kananan shekaru ta bayyana adadin yaran da ta haifa yayin da ta cika shekaru 28 a duniya.

A bidiyon da aka yada a TikTok, ta kira daya bayan daya dukkan ‘ya’yanta domin shiga bidiyon, inda kuma tace daya daga cikin ‘ya’yan da ta haifa ya bar duniya.

Matar da ta bayyana a matsayin mai aiki a kamfanin inshoran rayuwa ta ce haihuwa da tarbiyar yaran bai taba zama mata wani kalubale na rayuwa ba.

Kara karanta wannan

Lallai Fa: Bidiyon Wata Santaleliyar Budurwa Tana Fama Da Shanu Ya Girgiza Intanet

Matar da ta haifi 'ya'ya 9, shekarunta 28 ta ba da mamaki
Wata Mata Ta Ba da Mamaki Yayin da Ta Ce Tana da Shekaru 28, Amma Ta Haifi ’Ya’ya 9 | Hoto: TikTok/@mzkora
Asali: UGC

Ya kuma bayyana shekarun dukkan ‘ya’yan nata, ta ce babban ciki shekraunsa 17 a duniya yanzu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jama’ar kafar sada zumunta sun yi mamaki tare da yaba yadda kuruciyarta take a jikinta har yanzu duk da haihuwa da yawa.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

xLizz:

"Lallai ma. Na zaci shekarunsu ne ban gane ta yaya suke rage shekaru?!?!”

ecathrynpl:

"Tana yara 9 kuma shekarunta 28. Kawai dai tana kyan jiki shekarunta 40 ko makamancin haka yanzu.”

Raz Arkz:

"Kawai abin da nake son sani shine ta yaya kika iya dasu duka... Ina da 2 kawai amma rike su da wahala ga tsada.”

Brittney Philbrick:

"Wayyo za ki iya kirga duka? Shekarunta ba 28 bane yanzu kam. Cewa take ta haifi dan autanta tana da shekaru 28 , ina taya wannan kyakkyawan zuri’a murna.”

Kara karanta wannan

Bayan Sun Shafe Shekaru 10 da Aure Harda Yara 2, Ma'aurata Sun Gano Cewa Iyayensu Daya

Wani yace:

"To wai kece uwar tasu????? Menene sirrin.”

Nocturnal:

"Cewa take ta haifi dan autanta tana da shekaru 28 bata ce ta shekaruntu 28 ba za ta shiga 39 ne nan kusa don Allah mutane ake mai da hankali a aji.”

M1998:

"Ya aka yi ta fi kuruciya kan ‘ya’yanta na ukun farko.”

Aure ne babban nasarar rayuwata

A wani labarin kuma, wata mata ta ce bata taba samun wani nasara na rayuwa ba da ya wuce aure da ta yi.

Ta ce ta sha wahala a lokacin da take waje, mutane sun sha yi mata maganganun da bata so, amma ta hakura.

Ta ce a yanzu ana mata kallon mutunci, ta fi karfin a yi mata maganar da ba za ta iya dauka haka siddan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel