An Ceto Mutum 6 Cikin Wadanda 'yan Bindiga Suka Sace a Filin Jirgin Kasan Edo

An Ceto Mutum 6 Cikin Wadanda 'yan Bindiga Suka Sace a Filin Jirgin Kasan Edo

  • Mutum shida daga cikin wadanda 'yan bindiga suka tasa keyarsu a filin jirgin kasan jihar Edo sun kubuta daga hannun miyagun
  • Gwamnatin jihar Edo ta tabbatar da ceto jama'ar inda tace daga ciki akwai tsohon mai shekaru 65 tare da wata mai jego da jinjiri
  • Kamar yadda takardar da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Litinin ta nuna, akwai yarinya mai shekaru 6, sai wasu yara biyu kanana 'yan gida daya

Edo - Gwamnatin jihar Edo ta tabbatar da cewa, mutum shida da aka yi garkuwa da su a farmakin da 'yan bindiga suka kai filin jirgin kasa da ke jihar an ceto su.

Yanzu-yanzu
An Ceto Mutum 6 Cikin Wadanda 'yan Bindiga Suka Sace a Filin Jirgin Kasan Edo
Asali: UGC

Gwamnatin jihar ta sanar da wannan cigaban ne a wata takarda da ta fitar a ranar Litinin kamar yadda jaridar TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Wani Mai Hannu a Garkuwa Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya, Ya Fara Bayani

Wadanda aka ceto sun hada da wani tsoho mai shekaru 65, mai jego da jinjirinta, yarinya mai shekaru shida da wasu yara biyu 'yan gida daya masu shekaru biyu da biya.

A ranar Asabar, 'yan bindiga sun yi garkuwa da mutane masu tarin yawa a filin jirgin kasa da ke karamar hukumar Igueben ta jihar Edo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda aka sace din an gano suna jira ne domin hawa jirgin kasan zuwa filin jirgi na Igueben da ke Warri da ke jihar Delta yayin da lamarin ya faru.

A kalla mutum 30 aka yi garkuwa da su a wannan lokacin.

"Muna da tabbacin cewa za a ceto sauran wadanda aka yi garkuwa da su saboda jami'an tsaro kwararru masu zummar aiki ne suke bibiyar masu garkuwa da mutanen."

- Cewar Chris Nehikhare, kwamishinan yada labaran jihar Edo a wata takardar da ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hukumar NRC Ta Rufe Tashar Jirgin Kasa da Yan Bindiga Suka Kai Hari

"A yayin da lamurra ke faruwa a dajika, ku tabbatar cewa za mu cigaba da ba ku bayanai kuma muna bukatar goyon bayan duk masu ruwa da tsaki ballantana kafafen yada labarai da su tsaya kan labarin da akwai tare da gujewa bada rahoton da zai kara tayar da hankulan iyalan wadanda aka sace suke cikin damuwa."

- Ya kara da cewa.

Tarihi ne ya maimaita kansa

A wani labari na daban, a watan Maris sin shekarar da ta gabata, waus miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kan jirgin kasa da ya debo fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna a garin Rijau.

Sun halaka fasinjoji masu yawa tare da yin garkuwa da wasu inda suka dinga karbar kudin fansa kafin su sako su daga bisani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng