Fasihin Gaske: Bidiyon Yaro Yana Aski Kamar Kwararren Ma’aski Ya Girgiza Jama’ar Intanet

Fasihin Gaske: Bidiyon Yaro Yana Aski Kamar Kwararren Ma’aski Ya Girgiza Jama’ar Intanet

  • Wani bidiyon hazikin yaro yana amfani da na’urar aski kamar wani kwararre ya girgiza jama’a a kafar sada zumunta
  • A bidiyon da aka yada a TikTok, an ga lokacin da yaron ke tsaye a gaban manyan mutane, inda yake nuna kwarewarsa a iya aski
  • Da suke martani ga bidiyon, jama’ar kafar sada zumunta sun shiga mamakin yadda yaron ya koyi aski cikin kwarewa

Wani dan karamin yaro ya ba jama’ar kafar sada zumunta mamaki yayin da ya nuna kwarewarsa a sana’ar aski.

Hazikin yaron ya bayyana a gaban jama’a, inda aka ga yana rike da injin aski kamar wani kwararren da ya jima yana aikin.

Jama’ar kafar sada zumunta sun shiga mamakin yadda yaron yake da manyance, da kuma yadda yake kwalkwale kawunan jama’a.

Yaro yana aski mai ban mamaki
Fasihin Gaske: Bidiyon Yaro Yana Aski Kamar Kwararren Ma’aski Ya Girgiza Jama’ar Intanet | Hoto: @teejayreal/TikTok
Asali: UGC

A bidiyon, an ga wani babban mutum na zaune ya yi masa kuri yana kallo yayin da shi kuwa ya natsu yake aikinsa ko a jikinsa.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Saki Zafafan Hotunan Gidan Kwano Da Ya Kera, Ya Saka CCTV da Kayan Alatu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a TikTok

@reaganmariodarko:

“Meye yasa da yawan masu aski ke bari wani irin aski. Ma’askin gobe mai tarin murdadden gashi.”

@fridayegodi1:

“Aiki mai kyau daga gareka saboda kai uba ne na kirki dake shajja’a yara masu tasowa.”

@chommybabby:

“Kai, yadda yake murda hannunsa abin ban sha’awa ne."

@someonepride244:

"Ku duba da kyau ko da gaske yaro ne fa ko kuma gunki ne ke yaudararmu.”

@user427391588352:

"Aje yaron nan ya fi wasu masu aikin.”

@damola_law:

"Yadda yake riki da injin askin ya bayyana komai. Kwararre ne.”

@pheminasky:

"Me yasa suka yi amfani d amai katon kai. Ai zai kashe kasuwa.”

Gabjejen namiji na tuka tuwo, mutane da yawa sun girgiza

A wani labarin kuma, mutane sun shiga mamaki yadda wani magidanci ya shiga sana’ar da ba tasa ba, yana tuka tuwo a rana yana hada zufa.

Kara karanta wannan

Namijin gaske: Bidiyon gabjejen namiji na tuka tuwo yana gumi ya ba mamaki

A bidiyin da aka yada, an ga lokacin da mutumin ke sanye da jamfa yana sharbar zufa a lokacin da ya yiw muciya rikon gwani.

Jama’ar kafar sada zumunta sun gaza hakuri, sun yi martani mai daukar hankali kan wannan lamari mai ban mamaki da suka gani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel