Alkali Ya Sa a Kamo Masa Dan Takarar Gwamnan PDP Na Jihar Akwa Ibom Bisa Laifuka 2
- Yayin da zabe ya karato, kotu ta ba da umarnin a kame wani dan takarar gwamna, Umo Eno na jam’iyyar PDP a jihar Akwa Ibom
- Ana zargin dan takarar gwamnan ne da aikata ha’inci da kuma wata badakalda da ke da akala wa dukiyar da ba tasa ba
- Ba wannan ne karon farko da aka umarci kama wani dan takara ba, an sha yin hakan a Najeriya
Wuse, Abuja - Kotun majistare da ke zama a Wuse zone 6 a babban birnin tarayya Abuja ta ba da umarnin kame Umo Eno, dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Akwa Ibom.
Eno, dan gaban goshin gwamna Udom Emmanuel na jihar ta Akwa Ibom, shine ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan jihar da aka gudanar a watan Mayun bara.
An ruwaito cewa, ya samu kuri’u 993 yayin da jumillar deliget-deliget na zaben ya kasance 1,018 a zaben na fidda gwani.
Ya lallasa abokan hamayyarsa a zaben ciki har da Onofiok Luke, wanda mambane ba majalisar wakilai da ya samu kuri’u biyu da kuma Bassey Albert, mamban majalisar dattawa da ya samu kuri’a daya kacal.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda shari’a ta kasance a kotun majistaren Abuja
A wata takarda da TheCable tace ta samo, mai shari’a a kotun majistare, Emmanuel Iyanna ya ba da umarnin a kame dan takarar gwamnan a ranar 23 ga watan Disamban bara.
A cewar takardar, ana zargin dan takarar gwamnan da aikata laifin ha'inci da rashin gaskiya da suka ke da alaka da wata dukiya.
Wannan na zuwa ne bayan da Edet Godwin Etim ya shigar da karar da ke kalubalantar dan takarar gwamnan; wata kara mai lamba CR/94/2022.
Majiya ta shaidawa TheCable cewa, tuni an yi zaman kotu, inda mai shari’a ya gamsu da hujjoji tare da umartar a kamo Eno tare da gurfanar dashi a gabansa, Platinum Post ta ruwaito.
An ce mai shari’an ya ba da wannan umarnin ganin yadda dan takarar ya gaza kawo kansa gaban kotu tun bayan fara maganar.
EFCC Na Neman ‘Dan takaran Sanata a Kano a kan Zargin Damfara
A wani labarin kuma, hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin kasa zagon kasa na neman AA Zaura bisa zargin damfara.
EFCC na neman Abdulkareem Abdulsalam Zaura ne bisa zargin ya yi wata damfara ta dala miliyan 1.3.
A A Zaura dai dan takarar sanatan APC a jihar Kano, kuma ya shahara a jihar ta Arewa maso Yamma.
Asali: Legit.ng