Na sha Wahalar Banza: Magidanci Ya Gane Duk Yaran da Matarsa ta Haifa ba Nashi Bane

Na sha Wahalar Banza: Magidanci Ya Gane Duk Yaran da Matarsa ta Haifa ba Nashi Bane

  • Wani mutumi 'dan Najeriya yaje dandalin soshiyal midiya, inda ya sanar da abun da ya gano cewa 'yan da yake dauka a nashi ba 'ya'yanshi bane
  • Mutumin, wanda sana'arsa nishadantarwa ne a Akwa Ibom ya bayyana yadda matarsa ta fallasa sirrin a ranar Juma'a, 6 ga watan Janairu
  • Yayi bincike mai zurfi, inda ya gano hirarrakinta da dadironta, wanda yake tunanin shi ne uban 'ya'yanta da asali

Soundcraft, wani 'dan Najeriya mai nishadantarwa dake zaune a Akwa Ibom, ya gano cewa bashi bane asalin mahaifin 'ya'yansa uku.

Mutumin cike da takaici ya nufi dandalin Facebook gami da bayyana mummunan labarin a safiyar yau, inda yake cewa, matarsa ta dubi tsabar idonsa a safiyar yau a gaban 'ya'yansu ta sheda masa.

Magidanci
Na sha Wahalar Banza: Magidanci Ya Gane Duk Yaran da Matarsa ta Haifa ba Nashi Bane. Hoto daga Soundcraft D Ritualist
Asali: Facebook

Ya koka game da yadda ya dauki tsawon lokaci har zuwa yanzu yana wahala, wanda hakan yayi kama da wani sakon gargadin kada a zargesa idan aka ga yaran na wahala a gaba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Matar Aure Tana Gaggawar Ba Miji Abinci a Baki Kada ya Makara Aiki ya Janyo Cece-kuce

Kamar yadda ya rubuta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Chab kawai yanzu ne na gano cewa ba ni ne mahaifin 'ya'yana ba... Mandu The Nsit Atai matar ta dubi tsabar idona da safiyar yau a gaban 'ya'yana cewa ba ni bane mahaifinsu na asali ba, kuma za ta kai su wurin asalin mahaifinsu. Makwabtan dake wurin sun cika da mamakin jin kalaman da ta amayar.
"Ni:- dama duk tsawon lokacin nan nayi wahala a banza kenan kai.
"A zahirin gaskiya, bai kamata in kawo wannan batun nan ba, amma ina yin hakan ne saboda irin ficen da nayi. Idan kuka ga 'ya'yana suna wahala gobe, kada wanda ya ga laifina saboda na san ba za ta iya daukar dawainiyar da nake dauka ba.
"Kaji tsoron NSIT ATAI MATA."

A wallafar da yayi daga bisani a Facebook, inda ya dora hirar WhatsApp din dake tsakanin matarsa da uban yaran ta wanda ta adana sunansa a wayarta a matsayin matar fasto.'

Kara karanta wannan

Imo: Tsohon Gwamna da Yaransa 2 Sun Kubuta daga Halaka, Ya Bayyana Yadda Lamarin ya Faru

Yayi alkawarin bayyanawa duniya sakamakon gwajin kwayar halitta da zarar yayi.

Martanin 'yan soshiyal midiya

EkponoudimAbasi Job ta ce:

"Ko wane ne ya fada maka haka, yana kokarin tarwatsa maka alakarka da jininka ne.
"Kada ka wani yi gwajin kwayar halitta ga wadannan...
"Ka natsu ka cigaba da rayuwa da 'ya'yanka".

Queen Prince Ekpenyong ta ce:

"Ina rokonka aboki na, kada ka dauki abun da ta ce da gaske. Kawai tana kokarin tada maka hankali ne, saboda irin yadda kake kaunar yaran.
"Ba ka ma bukatar gwajin kwayar halitta don tabbatar da 'ya'yan naka ne, wadannan yaran basa da bambanci da kai. Ka share ta, neman ka tanka take."

Ekamma Udoh ta ce:

"Kada ka bari wani abu yasa ka rasa alaka mai kyau tsakaninka da yaran nan da suke kama da kai, duk irin barazanar da za a yi maka.

Kara karanta wannan

Shin suna zubewa? 'Yan Najeriya suna ta wanke sabbin Naira don gwada ingancinsu

"Ina rokonka kada ka bari 'ya'yan nan su taso ba tare da mahaifinsu ba, ka san cewa yaran naka ne, saboda haka a manta kawai. Mu mata muna maganganu idan mun fusata."

Gabriel Okonson ya ce:

"Idan haka ta ce, kasa a kamata ta rattaba hannu idan 'ya'yanka suka bace, za ta dandana kudarta. Idan ta tsaya kan bakar kai ba mahaifin 'ya'yan bane, ta biya kudin gwajin kwayar halitta, sannan idan sakamakon ya tabbatar kai ne mahaifinsu, ka maka ta kara kotu don bacin suna, sheganta maka 'ya'ya, da sauransu."

Sai ka maida ni ciki, jariri ya cafke hannun likitan da ya karba haihuwarsa

A wani labari na daban, wani jinjiri ya cafke hannun likitan da ya karba haihuwarsa inda ya ki sakinsa.

Jama'a da dama sun yi martanin cewa, yaron bai so aka haife shi a kasar da aka haife shi bane, shiyasa ya rike likitan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng