An Ci Gaba da Sauraron Shari'ar Yar Gidan Ganduje Da Mijinta

An Ci Gaba da Sauraron Shari'ar Yar Gidan Ganduje Da Mijinta

  • A kwanakin Baya ne dai Asiya Balaraba ta shigar da karar mijinta a gaban kotu kan a raba aurensu da mijin nata
  • Auren wanda suka shafe shekaru 16, Asiya na son ganin an datse shi sakamakon wasu korafe-korafe da ya turnuke su.
  • Gwamnatin jihar kano dai ta samu sabani da mijin Asiyan mai suna Inuwa Uba wanda har ta kai da gwamnatin ta rufe masa kamfaninsa

Kano - An ci gaba da sauraron karar da yar gidan gwamnan jihar Kano ta shigar gaban kotu kan a raba aurenta da mijinta. Rahoton wakilin Legit.ng

Mai Shari’a Abdullahi Halliru ne ya jagoranci zaman a karo na biyu kamar yadda ya jagoranceshi a zaman farko.

To sai dai zaman ba kamar na baya ba a wannan karon lauyoyi ne suka wakilici wanda ake kara da wanda yake kara a gaban kotun.

Kara karanta wannan

BUK: Dalibai Mata Sunga Tasku, An Shiga Har Dakunan Kwanan Su Anyi Musu Sata

Ganduje
An Ci Gaba da Sauraron Shari'ar Yar Gidan Ganduje Da Mijinta Hoto: Daily Nigeria
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tunda fari dai lauyan wanda ake kara Barista Umar I Umar ya gabatarwa da kotu wani korafi a rubuce cikin takarda inda yake kalubalantar wanda suke karar tasu. lauyan wadda take kara ya krbi takardar kuma ya ce a bashi lokaci su nazarceta.

Yanzu dai an daga shari'ar zuwa kwan Bakwai masu zuwa wato sai ranar 12 ga watan daya dan ci gaban wannan shari'ar.

Yaushe Yar Gidan Ganduje Ta Shigar da Mijin Nata Kara?

A ranar 23 ga watan Disamban shekarar bara, Asiya Balaraba ya ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ta shigar da mijin ta kara mai suna Inuwa Uba gaban kotu kan a raba aurensu wanda ya shafe shekaru 16.

To sai dai lokacin da Asiya tai da'awar mijin ya tubure tare da nuna cewa shi yana son matarsa kuma suna zaman aure cikin luman.

Kara karanta wannan

Yan Daba 61 hulumar yan sandan Jihar Kano Tayi Hole Kan Yunkurinsu Na Tada Tarzoma

A lokacin zaman kotun na wancan lokacin mai shari'a Halliru Abdullahi ya bukaci da yan jaridu da sauran mutane su basu waje dan yin shari'ar a sirri.

ALkalin kotun ya daga Shari'ar zuwa ranar 5 ga watan Janairun wannan shekara da zaummar su ma'auranta su samu su yi sulhu da junansu.

Anyi Sulhun?

To sai dai a zaman kotun da aka gudanar a ranar 5 ga watan nan ba'aga keyar daya daga cikin ma'aurantan ba sai dai lauyoyinsu wanda suka wakilcesu kuma suka bayar da bayanai akan su.

Jaridar Legit.ng Hausa zata kawo muku yadda zata kaya a zaman kotun da za'a gudanar anan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel