Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mai Gidan Otel a Jihar Oyo
- An ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wani manomi kuma mai gidan otal a Oyo
- Mazauna yankin da lamarin ya faru sun bayyana bukatar a gaggauta daukar mataki kan yawaita satar jama’a
- Ana yawan samun mutane a Najeriya, jami’an tsaro suna ci gaba da dauki ba dadi da ‘yan ta’adda a fadin kasar
Jihar Oyo - Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wani mai gidan otal, Mr. Dejo Ajuwon, Omoloju a yankin Iseyin a jihar Oyo.
Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, an sace mutumin ne a gonarsa da ke kauyen Serafu da ke kusa da titin Moniya-Iseyin a jihar.
A cewar majiyar tsaro da ta tattauna da Vanguard a ranar Alhamis, wannan ne karo na biyu da aka sace mutane a yankin a kasa da watanni biyu.
An kuma ruwaito cewa, an sace wani abokin wani gona da ke yankin a watan Disamban bara, kuma an biya kudin fansan da ya kai Naira miliyan biyu kafin a sako shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An ce Mr Ajuwon ya kaura ne zuwa Iseyin, wanda nan ne garinsu bayan da ya yi ritaya daga aiki, inda ya fara sana’ar noma da kuma harkar otal na tsawon shekaru 10.
Mazauna sun nemi a dauki mataki
Mazauna yankin dai sun shiga damuwa, sun kuma kalubalanaci ‘yan sanda da jami’an sojoji da su tabbatar da wanke kauyen Serafu daga ayyukan ‘yan ta’adda.
Hakazalika, sun bukaci jami’an tsaro da su yi amfani da bayanan sirri domin tabbatar da kakkabe kauyukan gefe daga barnar ‘yan bindiga da masu sace mutane.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu wata tattaunawa tsakanin masu garkuwan da kuma ahalin wanda suka sace balle neman kudin fansa, The Chronicle Newspaper ta ruwaito.
An yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adewale Osifeso, amma hakan ya ci tura, domin lambarsa ba ta shiga.
'Yan bindiga sun tare a wani dajin Bauchi, 'yan sanda sun sheke da yawa, sun kawo wasu
A wani labarin kuma, wasu 'yan bindiga sun tare a wani dajin jihar Bauchi, amma sun gamu da azababben farmakin 'yan sanda.
An bayyana yadda aka kashe 'yan bindiga tare da kwato makamai masu illa, kana an kama wasu 'yan bindiga.
Ana ci gaba da samun nasara kan 'yan bindiga, kana suna ci gaba da sace mutane a bangarori daban-daban na kasar nan.
Asali: Legit.ng