Daga Reno: Uwa Ta Nuna Halin Da Ta Riski Diyarta a Ciki Bayan Ta Nemi Mijinta Ya Kula da Diyarsu

Daga Reno: Uwa Ta Nuna Halin Da Ta Riski Diyarta a Ciki Bayan Ta Nemi Mijinta Ya Kula da Diyarsu

  • Wata matar aure ta caccaki mijinta mai ban dariya wanda ya goya diyarsu a bayan butun-butumi
  • Yayin da take wallafa bidiyon a TikTok, matar ta ce ta fita unguwa don haka ta nemi mijijta ya tayata renon diyarsu
  • Da yake kare kansa mijin ya ce yarinyar na fitina ne don haka ya goya ta a bayan butun-butumi

Wani bidiyon ban dariya na dan Najeriya da goya diyarsa a bayan butun-butumi ya ba mutane mamaki a soshiyal midiya.

Matar mutumin ta fita unguwa don haka ta bar masa diyarsu ya yi reno har zuwa lokacin da za ta dawo.

Yarinya goye a bayan butun-butumi
Daga Reno: Uwa Ta Nuna Halin Da Ta Riski Diyarta a Ciki Bayan Ta Nemi Mijinta Ya Kula da Diyarsu Hoto: @onyinye3/TikTok
Asali: UGC

Sai dai kuma, mutumin ya goya diyar tasa a bayan butun-butumi a lokacin da ta taso shi gaba da rigima.

Ya kuma bayyana cewa shi ba zai iya goya yarinyar ba don haka ya goya sa a bayan butun-butumi.

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Kama Hauka Tuburan a Abuja, Ta Nemi Wata Angela Ta Rabu da Mijinta, Bidiyon Ya Yadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jinjinawa butun-butumij a kan wannan aiki mai kyau da ta yi sannan ya ci gaba da yiwa yarinyar wasa yana kiranta da gimbiyarsa sannan ya bukace ta da lada ta motsa.

Ya ce:

"Wato matata bata nan, sannan ta bar ni da diyarmu kuma tana ta damuna. Ban san yadda ake goyo ba don haka dole na goyata a bayan wannan abuj, akalla wannan butun-butumin ya yi gagarumin aiki.
"Ya ke gimbiyata. Idan mahaifiyarki ta dawo kooo, ina fatan ba za ta kashe ni ba fah. Ina kaunarki mhuaa. Kada ki kitsa!! Kada ki motsa!!"

Da take martani ga bidiyon, matarsa ta wallafa shi a TikTok da taken:

"Ku ga abun da mijima ya yiwa diyarmu lokacij da bana gida. Wani irin uba ne kai?"

Jama'a sun yi martani

Tima Cham ta rubuta:

"Fuskarta ya yi kaman idan mahaifiyata ta zo sai na fada mata komai."

Kara karanta wannan

Shekarun Diyata 4 Kacal: Magidanci Dan Shekaru 50 Ya Koka Kan Rashin Aure Da Wuri

Mama Banke ta yi martani:

"Baiwar Allah a bayan butun-butumi mai sanyi."

Naebae ta yi martani:

"Ta yaya mutumin nan ya goya yarinyar nan a bayan butun-butumin. Da ya yi amfani da karfin da ya yi amfani da shi wajen goyata a bayansa."

Domonique ta ce:

"Toh idan butun-butumin ya fadi fa."

Kalli bidiyon a kasa:

A wani labari na daban, bidiyon wata mata tana hauka tuburan a yankin Jahi da ke Abuja ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

An gano matar tana ambatan wata mai suna Angela tare da umurtanta a kan ta bar mata mijinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel