Legas Ta Cika da Cunkoso Yayin da Mai Mota Ya Banke Dan Sanda, Ya Yi Fecewarsa
- Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta yi Alla-wadai da yadda wani direba ya banke dan sanda, ya raunatashi kana ya tsere
- An yada wasu hotuna na yadda dan sanda ya samu mummunan rauni bayan da aka buge shi a wani yankin jihar
- Ya zuwa yanzu ana ci gaba da bincike, kuma hukumar ta ce sam wannan ba abu ne da ya kamata yake faruwa na
Jihar Legas - An samu hargitsi a yankin Ilubinrin na gadar Third Mainland da ke jihar Legas yayin da wani mai mota ya banke dan sanda, ya raunata shi ya tsere.
An tattaro cewa, wannan lamari ya haifar cunkoso a kan gadar a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar SaharaReporters ta tattaro.
Hotunan da hukumar ji da cunkoso ta Legas (LASTMA) ta yada a Twitter sun nuna yadda dan sandan ya samu raunuka masu yawa a jikinsa; fuska da hannu, jini na zuba.
Rubutun da LASTMA ta yada ya ce, buge dan sandan ya jawo cunkoso, kana mutane da yawa sun taro don ganewa idonsu abin da ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, an ce tuni aka sanar da hukumar LASAMBUS domin shiga lamarin, kuma har yanzu ana ci gaba da bincike.
Martanin hukumar ‘yan sanda
Da yake martani ga abin da ya faru, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ya yi Alla-wadai da wannan barna da ta kai ga illata jami’in dan sanda.
Ya yi martani ga hotunan da LASTMA ta yada tare da cewa:
“Mintuna 35 amma kuma sau 7 kadai aka yada a Twitter.
“A juya wannan, a ce motar ‘yan sanda ce ta buge wani ta gudu ku ga yadda za a yada a Twitter na kakkautawa.
“Irin haka dai a kullum ake wufantar da aikin kirki na ‘yan sanda, ake yada karyata akansu na munin aiki da gangancinsu.”
Dan sanda ya kashe lauya a jihar Legas
A tun farko kun ji yadda Legas ta dauki zafi bayan da wani dan sanda ya bindige wata lauya matar aure mai dauke da juna biyun wata bakwai.
Kafafen sada zumunta sun bayyana jama’ar kasar nan suka yi ta martani kan wannan lamarin da ya dauki matukar hankali.
Ba wannan ne karon farko da ake samun ‘yan sanda ke kashe fararen hula ba a Najeriya, hakan ya sha faruwa.
Asali: Legit.ng