EFCC ta Fallasa Cuwa-Cuwar Naira Biliyan 13 a Harkar Tallafin Fetur a Shekaru 5

EFCC ta Fallasa Cuwa-Cuwar Naira Biliyan 13 a Harkar Tallafin Fetur a Shekaru 5

  • Binciken hukumar EFCC ya nuna yadda aka biya kudi babu gaira babu dalili da sunan tallafin fetur
  • Badakalar Naira biliyan 13 aka tafka tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021 da sunan biyan tallafin mai
  • Kamfanoni su na cuwa-cuwa iri kama daga wajen hako danyen mai zuwa wajen saida fetur a kasar

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya ta gano kimanin N13bn a matsayin kudin karya da aka biya kamfanoni da sunan tallafin man fetur.

Rahoton Punch ya nuna cewa an biya wadannan makudan kudi ne tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021 a lokacin da gwamnati take daukar nauyin tallafin.

EFCC da take da nauyin yin bincike da hukunta badakalar tallafi mai da gas a Najeriya ta gano N12,998,963,178.29 da aka karkatar wajen biyan kudin bogi.

An yi haka ne a lokacin da ake biyan tallafi tsakanin shekarar 2017 da ta 2021.

Kara karanta wannan

Arewacin Najeriya Zai Zama Dubai, Ana Neman Danyen Man Fetur a Wasu Jihohi

Abin da aka sace a duk shekara

A shekarar 2017, jami'an EFCC sun gano N4.7bn, sai N4.29bn a shekarar 2018, N2.41bn a 2019, a shekarar 2020 an bankado N416.51m, sai N1.22bn a shekarar 2021.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Post ta ce rahoton da aka fitar ya nuna ana tafka badakala a harkar mai da gas a Najeriya.

Fetur
Tankan man Matrix Hoto: matrixenergygroup.com
Asali: UGC

Akwai damar da za a sulale da biliyoyi ba tare da an farga ba tun daga hako danyen mai domin ba a san adadin gangunan da ake samu a kullum ba.

Baya ga haka, ‘yan fasa-kauri su na sace arzikin Najeriya daga bututun mai. Ko bayan an tace man fetur, akwai masu sulalewa da shi daga gidajen mai.

Ana dauke fetur a kai kasashen makawabta

Baya ga satar fetur da aka yi idan ya shigo Najeriya, akwai wadanda ke gurbata man domin neman kudi, wasu kuma su na fita da su zuwa kasashen waje.

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran APC, Tinubu Ya Dage Sai Ya Cire Tallafin Fetur Idan Ya Gaji Buhari

Rahoton Hukumar EFCC ya nuna idan ba a magance wadannan matsaloli da ake fama da su ba, za su yi wa tattalin arzikin Najeriya mummunar illa.

Ana tsallakawa da motocin mai zuwa wasu jihohin ko yankuna, har a kai su makwabtan Najeriya domin za a fi samun riba idan aka saida su a waje.

A Agustan 2019 da NSA ya yi bincike a iyakokin kasar, an gano wasu motoci da ke dakon man Najeriya a kasashen makawabta, sun je saida fetur da tsada.

Lantarki ya kara tsada

Ba tare da an yi wa mutane bayani ba, rahoto ya zo cewa an wayi gari kurum an fahimci kamfanonin DisCos duk sun kara kudin sayen wutar lantarki.

Wannan kari da aka yi a sabuwar shekara ta 2023 ba shi ne na farko ba, a Fubrairun 2022 sai da hukumar NERC ta bada sanarwar yin karin 5-12% a ko ina.

Kara karanta wannan

2022: Wasu manyan abubuwa 10 da suka faru a 2022, sun ja hankalin jama'a a duniya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng