Abinda Ya Sa Ba Zan Iya Soyayya Da Namijin Da Ba Zai Rika Kwanciya Dani Ba, Jaruma

Abinda Ya Sa Ba Zan Iya Soyayya Da Namijin Da Ba Zai Rika Kwanciya Dani Ba, Jaruma

  • Fitacciyar Jarumar Shirin Fim a Najeriya ta girgiza mutane inda ta bayyana irin soyayyar da zata iya yi da wacce ba zata yi ba
  • Nkechi Blessing, Jaruma a masana'antar Nollywood da ke kudancin Najeriya tace ba zata zauna da Namijin ba zai rage mata zafi ba
  • Tace jin dadin juna a soyayya yana da dadi don haka ba za'a ga kafarta a soyayyar da babu wannan holewa ba

Jaruma a masana'antar shirya Fina-Finai Nollywood dake kudancin Najeriya, Nkechi Blessing, ta bayyana ra'ayinta kan batu mai rudarwa da ake tattauna wa a Soshiyal midiya.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa da take tsokaci kan batun na kaurace wa saduwa da juna, Jarumar Fim din ta ce ba za'a ga kafarta a kan wannan layin ba.

Jaruma Nkechi Blessing.
Abinda Ya Sa Ba Zan Iya Soyayya Da Namijin Da Ba Zai Rika Kwanciya Dani Ba, Jaruma Hoto: Nkechi Blessing
Asali: UGC

Blessing ta ba da misali da cewa mutane ba zasu sayi Mota ba tare da sun ɗana ba ko kuma ba zai yuwu a sayi Tsire ba, ba tare da mai sayen ya ɗanɗana ba.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Bayyana Wanda Zai Ci Zaben Shugaban Kasa Na 2023 A Najeriya

Jarumar ta bayyana cewa jima'i yana da dadi kuma a ra'ayinta ba zata iya zama ba tare da wanda suke tare yana rage mata zafi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamanta, jarumar Nollywood din ta ce:

"Wannan ba inuwar hutawar kowa bace, idan za'a sayi Mota ana hawa a ɗana don gano ko Injin Motar mai kyau ne, haka idan zaka sayi Naman tsire ana saf daya na dandano."
"Zancen soyayya kam ba da ni ba, abun nan yana da daɗi fa, ba zan zauna a irin wannan soyayya ba ko kadan, ba dai dani ba."

Wannan batu dai ya ja hankalin mutane da yawa a soshiyal midiya yayin da wasu ke ta fadin na su ra'ayoyin da abinda zasu iya aikata wa a soyayya.

Budurwa Ta Sha Alwashin Lallasa Mahaifinta Kan Kawo Abokiyar Sharholiyarsa Gida

A wani labarin kuma Wata Budurwa ta yi barazanar hukunta mahaifinta kan kawi abokiyar cin kashinsa har cikin gida

Kara karanta wannan

Bidiyon Matar Aure Tana Gaggawar Ba Miji Abinci a Baki Kada ya Makara Aiki ya Janyo Cece-kuce

Kamar yadda aka gani a bidiyon, mutane sun yi kokarin tausar fusatacciyar matashiyar sannan sun janye ta daga tunkarar dattijon mutumin.

An jiyo wasu yan uwansu suna gargadinta kan idan ta isa ta daura hannunta a kan dattijon yayin da sauran ke kare mahaifin nata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262