An Maka Kamfanin Twitter a Kotu Saboda Gaza Biyan Kudin Haya

An Maka Kamfanin Twitter a Kotu Saboda Gaza Biyan Kudin Haya

  • Mai ginin daya daga cikin ofishoshin Twitter ya fusata, ya tafi kotu saboda Elon Musk ya ki biyan kudin haya
  • Mai ginin, wanda ya kai kara a ranar 16 ga watan Disamba ya ba Twitter kwana biyar ko kuma kamfanin ya fuskancu fushin doka
  • Rahotannin sun ce, karar bata shafi hedkwatar Twitter ba, kawai dai ya shafi daya daga ofisoshin ne da ke San Francisco

An maka kamfanin Twitter a kotu bisa gaza biyan kudin da kuma karya doka da ka'idar da aka yi na bashi hayar ofishi a birnin San Francisco na kasar Amurka.

Wannan kara dai ta shafi ofishin Twitter ne da ke lamba 650 a titin Califonia, bai shafi hedkwatarsa da ke titin Market ba, inji rahoton CNN.

Wannan batu na zuwa ne bayan da aka ruwaito cewa, a watan Disamba Elon Musk ya ki biyan kudin hayan ofisoshin Twitter a fadin duniya, ciki kuwa har da hedkwatarsa.

Kara karanta wannan

Duk da Albashin Naira Biliyan 2 a Wata, Akwai ‘Dan Wasa 1 da Ya Sha Gaban Ronaldo a Kudi

Musk ya ki biyan kudin haya, an maka shi a kotu
An Maka Kamfanin Twitter a Kotu Saboda Gaza Biyan Kudin Haya | Hoto: Anadolu Agency / Contributor
Asali: Getty Images

Bayan sayen Twitter, Musk na ta jawo cece-kuce

Musk, wanda shine sabon mai kamfanin Twitter ya kuma umarci ma'aikatansa da kada su biya duk wani mai kawo kaya kamfanin a yunkurinsa na rage kashe kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kwafin takardar karar da aka cike a makon da ya gabata a babban kotun Califonia da ke San Francisco, an ce ana bin Twitter kudin hayan da ya kai $136.260, kusa N60,635,700 na ofishinsa da ke 650 titin Califonia.

Wannan kudi da ake bin Twitter ya kai ga mai ginin ba da wa'adi ga kamfanin a ranar 16 ga watan Disamba, inda aka ba kamfanin kwanaki biyar ya biya kudin.

Abin da mai ginin ke bukata

Karar ta kuma roki kotu cewa, dole ne Twitter ya biya hayan hade da kudin ruwa da ma kudin biyan lauyoyin da aka dauka.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Kasar Larabawa ta cire haraji kan barasa, ta amince a sha giya da rana a Ramadana

Ya zuwa yanzu dai babu wani martani daga Twitter ko dillalin ginin da kamfanin yake na yadda aka kaya.

A cewar rahoton na CNN, lauyoyin gine-gine sun ce, wannan kara za ta shafi wasu wurare idan Elon Musk ya gaza biyan kudin hayan ofisoshin Twitter.

A karar ta makon jiya, an ce kotun na da damar korar Twitter a ginin tare da kakaba mata biyan abin da mai kara ya shigar, amma an ce mai ginin yana martaba Twitter.

Idan baku manta ba, attajirin mai kudin duniya Musk ya siya Twitter a kan farashin $44bn a watan Oktoban da ta gabata, kuma ya gaji bashi mai tarin yawa da zazi biya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.