Gabjejen Namiji Ya Sharbi Zufa Yayin da Yake Tuka Tuwo, Bidiyonsa Ya Shiga Duniya
- Wani mutum ya sha yabo a matsayin mijin kirki bayan da bidiyonsa ya nuna yadda yake tuka tuwo
- An ga lokacin da ya jike da zufa sharkaf yayin da yake tuka tuwo a rana, saman jamfarsa ta jike da zufa
- Yadda yake tuka tuwon cikin salo ya ba mutane mamaki, da yawa suna ta mamaki tare da kirsan na namijin gaske
‘Yan TikTok sun yabawa wani mutumin da aka gani yan tuka tuwo cikin salo mai ban mamaki, da karfinsa.
Kakkarfan mutumin ya rike muciya cikin salo, yana tuka tuwa ga kuma yana ta hada zufa kamar mai dakon siminti.
Duba da bayansa, an ga jamfarsa ta jike sharkaf da zufa a lokacin da yake tuka tuwon a cikin rana.
Daga yadda yake juya muciyar, a bayyane yake ba wannan ne karon farko da yake tuka tuwo ba, kwararre ne a fannin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bidiyon namiji da tuka tuwo ya ba da mamaki a kafar sada zumunta
Mutane da yawa a kafar TikTok sun yi martani mai daukar hankali, inda suka yi ta yaba masa da yin irin wannan aikin,
Ya zuwa ranar 1 ga watan Janairu, bidiyon da @user4118480046733 ya yada ya samu dangwalen mutane sama da 6.9k.
Kalli bidiyon:
Martanin jama'a
Legit.ng Hausa ta tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa bayan ganin wannan bidiyo mai daukar hankali. Ga kadan daga ciki:
@adamandaratu795 yace:
"Ka yi komai dan uwana. Zan kawo maka kyauta karshen shekarar nan."
@Nana Owusu korkor yace:
"Wannan shi ake kira namijin gaske."
@Samson Yohanna400 yace:
"Aiki mai kyau dan uwa."
Yara Sun Ga Bature Ido da Ido a Karon Farko, Sun Shiga Mamakin Kyawun Jikinsa
A wani labarin kuma, an yada bidiyon wani baturen da ya kai ziyara gidan bakaken fata, ya gamu da yara kanana da suka binciki halittar jikinsa.
A bidiyon, an ga lokacin da yaran ke cewa, jikinsa ya yi musu kyau, kuma sun tambayi me yasa fatarsa ta bambanta da tasu.
Wasu yaran kuma sun lallatsa gashin kansa, sun ga yana da laushi ba kamar na bakaken fata ba, sun higa mamaki. Jama'ar kafar sada zumunta sun yi martani.
Asali: Legit.ng