Yan Bindiga Sun Kashe Jigon PDP da Wasu Uku a Jihar Anambra

Yan Bindiga Sun Kashe Jigon PDP da Wasu Uku a Jihar Anambra

  • Mahara sun halaka wasu mutane hudu a yankin Awka da ke jihar Anambra ta hanyar bindige su
  • Yan bindiga sun shiga harabar wani gida sannan suka Kenechukwu Okeke wanda yake jigo ne na PDP da wasu mutum uku
  • Zuwa yanzu, rundunar yan sandan jihar Anambra ta ce bata samu rahoton lamarin ba a ofishinta

Anambra - Jaridar Sahara Reporters ta rahoto cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kashe mutane hudu a garin Awka, babban birnin jihar Anambra.

Majiyoyi sun kawo a ranar Talata, 3 ga watan Disamba, cewa kazamin harin ya afku ne a harabar gidan wani Cif Obi Maduka a yankin Nodu Okpuno.

Jihar Anambra
Yan Bindiga Sun Kashe Jigon PDP da Wasu Uku a Jihar Anambra Hoto: Punch
Asali: UGC

An tattaro cewa daya daga cikin wadanda abun ya ritsa da su mai suna Kenechukwu Okeke, ya kasance shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a yankin.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Shugaban Jam'iyyar PDP Yankan Rago a Jihar Arewa

An rahoto cewa yan bindigar sun isa gidan ne a wata motar Toyota Corolla sannan suka harbe mutane hudu da ke zaune a harabar gidan sannan suka gudu suka barsu kwance cikin jini,

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daya daga cikin majiyoyin ya bayyana sunayen wadanda aka kashe a matsayin Onyiebo Okoye aka Onwa, Kenechukwu Okeke (shugaban PDP), Jude Ebenezer da Obinna Maduka.

An jiyo daya daga cikin mutanen da suka hallara a wajen da mutanen da aka bindige suke kwance yana cewa:

"Wannan na da sauran numfashi, mu dauke shi mu kai shi asibiti."

A halin da ake ciki, wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa yan bindigar sun bi wani ne cikin harabar gidan da mutanen ke zaune, kuma da suka kasa kama wanda shine burinsu, sai suka bude wuta a kan mutanen da ke zaune suna hirarsu.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Kama Yahoo Boys Da Suka Sace Abokin Aikinsu Don Ya Hana Su Kasonsu Cikin N22m Na Zamba

Da take martani a kan lamarin, rundunar yan sandan jihar Anambra ta bayyana cewa har yanzu bata samu kowani rahoto a kan kisan ba.

Kakakin rundunar, DSP Tochukwu Ikenga, ya yi kira ga yan uwan mutanen da su je ofishin yan sanda don kai rahoton lamarin, Nigerian Tribune ta rahoto.

Ikenga ya ce:

"Bani da labarin rahoto mai kama da wannan a gabana, ina mai umurtan shaidun lamarin ko yan uwan mutanen da su gabatar da jawabin da zai taimakaa yan sanda don gudnar da bincike."

A wani labari na daban, dakarun rundunar sojin saman Najeriya sun sheke mayakan kungiyar Boko Haram 30 ciki harda manyan kwamandojinsu guda uku sannan sun jikkata wasu 40.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng