Na Zaci Na Mutu, Inji Tsohon Gwamnan Da ’Yan Bindiga Suka Kai Wa Mummunan Hari
- Jim kadan bayan tsallake rijiya da baya, tsohon gwamnan jihar Imo ya fito ya yi magana kan abin da ya faru
- A cewarsa, ya zaci tuni ya zama gawa lokacin da 'yan bindigan suka kai masa harin da ya kashe mutanensa hudu
- Ana yawan samun hare-hare kan masu rike da mulki ko tsoffin masu mukamai a kasar nan, musamman shekarar da ta gabata
JIhar Imo - Tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim ya yi magana bayan da ‘yan bindiga suka kai masa farmaki a ranar Litinin 2 ga watan Janairu, inda suka kashe ‘yan sandan da ke tare dashi har mutum hudu.
Tsohon gwamnan ya tsallake harin da aka kai masa duk da ruwan alburusai da aka yi a kan motarsa a yankin karamar hukumar Ehime Mbano ta jihar Imo, PM News ta ruwaito.
Ohakim ya shaidawa manema labarai cewa, ya tsallake rijiya da baya bisa kariyar ubangiji ta musamman da kuma muta mai sulke da yake cikinta.
Yadda lamarin ya faru, ta bakin tsohon gwamna
Ya bayyana cewa, ya zaci sunansa matacce a lokacin da ‘yan bindigan suka fara ruwan wuta kan motar tasa, gashi yana tare bda ‘ya’yansa biyu lokaicn da lamarin ya faru.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
“Muna tuki ne a tsakanin Isiala Mbano da Ehime Mbano. Wadannan mutanen sun tare mu ne a wani wuri da ake kira Umualumaku.
“Sun farmake mu ta baya kuma suka yi ta wuta kan motocinmu babu kakkautawa. Na za ci na riga da na mutu kuma gashi ina tare da ‘ya’yana biyu – da na da diya ta.
“Abin da ya kubutar dani mota ce mai sulke. Cewar ina raye a yau nufi ne na musamman daga Allah da kuma mota mai sulke.”
Abin takaici: An kashe jami'ai hudu
Tsohon gwamnan ya kuma koka da cewa, an kashe masa jami’an tsaron ‘yan sanda hudu a lokacin, ciki har da direbansa.
Ya kuma ce wadannan 'yan bindiga kwararrun masheka ne masu horo ba wai kananan 'yan daba bane, inji rahoton Vanguard.
Ya kara da cewa:
“Tabbas, mun yi rashin yaranmu hudu kuma na ji babu dadi. Ta yaya hakan zai faru? Wane laifi suka aikata?”
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa, ‘yan bindigan sun bi su, sun ci gaba da harbi kan tayun ababen hayansu, inda yace sun yi sa’ar tsira da fasassun tayu har zuwa gida.
Daga karshe ya ce gwamnatin jihar Imo ta tabbatar da daukar gawarwakin wadanda suka mutu domin jana’izarsu a nan gaba.
A shekarar da ta gabata ne wasu tsagerun 'yan bindiga suka kai farmaki kan ayarin mataimakin gwamna a jihar Kebbi.
Asali: Legit.ng