Wani Mutumi Ya Ziyarci Gidan Tsohuwar Matarsa, Ya Kama Tube Kaya a Gaban 'Ya'Yansa a Bidiyo
- Wata budurwa ta wallafa bidiyon yadda wani abun mamaki ya faru da mahaifinta lokacin da ya ziyarci mamarsu duk da sun rabu
- A bidiyon an ga magidancin na nuna jin dadi bayan ya shiga dakin tsohuwar matarsa
- Da farko mutumin wanda ke cikin farin ciki ya fara yabon dakin tsohuwar matar daga bisa ya fara cire kaya a gaban yaransa
Wata budurwa ta shirya shagalin haduwar iyalai bayan mahaifinta da mahaifiyarsa sun rabu da juna ba da jimawa ba.
An shirya taron a gidan da mahaifiyar ke zaune kuma kowa ya yi mamakin abinda ya faru lokacin da magaidancin ya iso wurin cikin doguwar riga fanjama.
Jim kadan bayan zuwansa wurin shagali, ya kalli kowane bangaren dakin tsohuwar matar tasa kana ya fara mata kalaman yabo bisa kokarinta wajen ƙawata dakin.
Kanwar Maza: Yadda Matashi Ya Kwanta a Bakin Gate Tare Da Garkame Shi Don Hana Maneman Auren Kanwarsa Shiga
Kai tsaye ya tafi ya fara kokarin zare tufafinsa, lamarin da ya jefa kowa dake wurin cikin yanayi na daban.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Diyarsa ta yi mamaki matuka yayin da ta kalli yadda mahaifinta ke kokarin tube kayansa. Ta tambaye shi meyasa zai yi haka ya ba ta masa da cewa, "Ina kokarin cire karamin wando na ne."
Da ta wallafa bidiyon a shafin sada zumunta TikTok, diyar mutumin ta ce:
"Iyaye na guda biyu sun rabu, amma mun shirya wani taro domin haɗuwa a yi zumunci a gidan mamata. A lokacin Baba ya zo cikin binjimemiyar riga domin ya shafe darensa a nan, meyasa babana yake kamar haka?"
Bidiyon yadda abun ya faru
Martanin jama'a kan lamarin
@rileyd198 ya ce:
"Irin har yanzun ke matata ce, matsa can."
@miafordays ya ce:
"Watau ya zo a shirye zai shafe dare a gidan, mutumin fa ya tuno tsohuwar soyayyar aure, ya shirya ba da rayuwarsa."
@mobrownin ya ce:
"Dama can yana jiran a gayyace shi, wurin ya yi kyau sosai. Mahaifiyarku tana da saukin kai."
A wani labarin kuma Wata Sabuwar Amarya ta shiga tashin hankali yayin da ta kama Ango na lalata da kanwarta a gado kwana huɗu da aurensu
Sabuwar amaryar da abun ya sosa wa zuciya, tace lamarin ya taɓa ta yadda ta koma Otal na tsawon mako ɗaya ba wanka da yawo don komai ba ya mata daɗi.
Haka zalika ta nuna ba zata taɓa yafe musu ba kuma ta garkame lambobin mahaifiyarta da surukarta saboda sun nemi ta kai zuciya nesa.
Asali: Legit.ng