Kasurgumin Shugaban ’Yan Bindiga Ya Tsere Yayin da Sojoji Suka Kashe Yaransa 16 a Zamfara

Kasurgumin Shugaban ’Yan Bindiga Ya Tsere Yayin da Sojoji Suka Kashe Yaransa 16 a Zamfara

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta yi nasarar fatattakar 'yan bindiga da yawa a jihar Zamfara, inji majiya
  • Shugaban 'yan bindiga, Gwoska Dankarami ya tsallake rijiya da baya, an lalata gidansa, an kashe masa mutane 16
  • Rundunar sojin saman Najeriya na ci gaba da kakkabe 'yan bindiga daga dazukan kasar nan, musamman Arewa

Zurmi, jihar Zamfara - Akalla ‘yan bindiga 16 ne aka hallaka a harin jirgin saman sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Hadarin Daji a wata maboyar tsageru a hanyar Kaura na Moda ta karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Hakazalika, yayin wannan aiki na sojin sama, an ce wani kasurgumin dan bindigan da aka dade ana nema, Gwoska Dankarami ya tsallake rijiya da baya, da kadan ya halaka.

A cewar rahoton da wakilin Punch ya samo a ranar Lahadi, Dankarami ya tsallake ya gudu ne yayin farmakin da sojoji suka kai a jajiberin sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

2023: Gaskiya Ta Fito, Gwamnan APC Ya Magantu Kan Rahoton Yana Yi Wa PDP Aiki

Sojin sama sun ragargaji 'yan bindiga, shugaban tsageru ya tsallake rijiya da baya
Kasurgumin Shugaban ’Yan Bindiga Ya Tsere Yayin da Sojoji Suka Kashe Yaransa 16 a Zamfara | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kasurgumin dan bindiga ya shiga damuwa

Rahoton na gidan soja ya bayyana cewa, wata majiya daga tsagin kasurgumin dan bindigan ta tabbatar da yadda Danrami ya firgita tare da koka yunkurin sojojin Najeriya na hallaka shi da iyalansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta bayyana cewa:

“An ji shi yana kokawa sosai game da farmakin na jajibirin sabuwar shekara, wacce ta dauki tsawon awanni, an kashe yaransa 16 tare da ruguza sabon gidan da ya gina da kuma maboyarsa."

Rahoton ya kuma bayyana cewa, Dankarami ya kadu da kuma shiga mummunan yanayi tun lokacin da jami’an sojan suka yi kokarin hallaka shi da tare da kulle tarihinsa, rahoton PR Nigeria.

Aikin sojin sama ne ragargazar 'yan bindiga

Lokacin da aka tuntubi kakakin sojin saman Najeriya, AC Edward Gabkwet ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce Dankarami da masu hali irin nasa ba za su tsira daga matakin soji ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso a Gusau Jihar Zamfara: Zan Ba Da Fifiko Kan Muhimman Abubuwa 2 Idan Na Ci Zaben 2023

Ya kuma bayyana cewa, babban manufar sojin saman Najeriya shine zakulowa tare da tabbatar da kakkabe ‘yan ta’adda a kasar.

A wani labari mai kama da wannan a jihar Borno, an hallaka wasu 'yan ta'addan Boko Haram yayin da sojin sama suka kai farmaki mai tsanani a mabiyar 'yan ta'adda.

An ruwaito yadda aka samu nasarar raunata 'yan ta'adda da yawa bayan daidaita mabiyarsu a Bama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.