Asibiti Sun Kwace Jaririya Sabon Haihuwa kan N383,500 da Iyayensa Suka Kasa Biya
- Wani asibitin kudi a Warri dake jihar Delta sun kwace sabuwar jinjira tsawon sama da wata daya saboda iyayenta sun gaza biyan kudin da asibiti ke bin su bashi
- An tattaro yadda babban asibitin Warri suka tura iyayen asibitin Unique Health Medical Center saboda karancin gadajen kwantarwa bayan matar ta haifi 'yan biyu
- Mahaifiyar jinjirar ta koka game da yadda asibitin suka murje ido suka ki bata 'diyarta, wacce ko sanyata a ido bata kara ba tunda suka kwace duk a kan bashin N383,500
Delta - Wani asibiti mai suna Unique Health Medical Center a Warri, cikin jihar Delta sun kwace sabuwar jinjira saboda gaza biyan kudin asibiti N383,500 da aka binsu bashi sama da wata daya.
Punch Metro ta tattaro yadda mahaifiyar 'yan biyun, Mrs Akpesiri Ojoko ta haifi 'yan biyu a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2022 a babban asibitin Warri.
An gano yadda aka garzaya da daya daga cikin 'yan biyun asibitin kudi daga babban asibitin saboda karancin gadaje.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin bayyana mummunan lamarin, Mrs Ojiko ta roki gwamnatin jihar Delta da masu hannu da shuni da su tallafa wajen biyan bashin asibitin don ta samu damar amsar jinjirarta.
A cewarta:
”Na haifi jinjiraye a ranar 17 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata, namiji da mace a babban asibitin Warri, amma hukumar asibitin ta shaida mana cewa babu gadon da za a kwantar da yaran kuma ba za su iya ajiya jinjiraye biyu a gado daya ba.
"Sun fara kiran wasu asibitoci don tura jinjirar amma muka ki saboda mun san wasu daga cikin asibitocin da suka ambata, hakan yasa muka shaida musu suna da tsada kuma ba zamu iya biyan kudinsu ba.
"Daga karshe, suka turamu Unique Health Medical Center a nan Warri, ba mu da wani zabi da ya wuce muje.
"Ya kamata a sallami jinjirar a ranar 27 ga watan Nuwamba, 2022, amma tunda mun gaza biyan kudin, asibitin suka kwace jinjirar har sai mun biya kudin kafin su sakar mana ita.
"Suna bin mu bashin N433,500 kafin 'yar uwata ta kawo N50,000. Mun biya N50,000 da 'yar uwata ta kawo, ya kamata mu cika N383,500 kafin a sakar min jinjirata.
"Jinjirata ta kai kusan wata daya da wasu makwanni da haihuwa amma ban kara sanya ta a ido ba yanzu wata daya kenan da suka kwaceta, ba sa bari na ganinta. Ina rokon gwamna Ifeanyi Okowa da sauran masu hannu da shuni da su agaza min"
Haka zalika, an tattaro yadda mahaifin jinjirayen, Mr Destiny Ojiko, matukin adaidaita sahu ya tsere da farko daga jin kudin da asibitin ke binsu na N433,500 saboda takaicin yadda yake ta neman agaji.
Yayin da aka tuntubi asibitin, likitan dake da aiki ya ce ba za a saki jinjirar ba har sai an cika N382,500.
Asibiti su rike matar makaho kan bashi
A wani labari na daban, wani asibiti ya rike matar wani makaho saboda bashin da suke bin su.
An gano cewa, a asibitin har jinjirinta ya mutu amma tsananin talauci yasa suka gaza biyan bashin da ake bin su.
Asali: Legit.ng