Hukumar asibiti ta damke matar makaho a kan kasa biyan N248,000

Hukumar asibiti ta damke matar makaho a kan kasa biyan N248,000

- Hukumar wani asibiti mai zaman kansa sun rike matar makaho kuma kurma a kan bashin N248,000

- Suna rike da ita na watanni 3, har jaririnta ya mutu a asibitin, tsabar talauci ya hana ta biyan bashin

- Matar ta roki gwamnatin jihar Anambra da Ebonyi, da duk wasu masu hali da su taimaka su biya mata bashin

Hukumar wani asibiti mai zaman kansa da ke Awka, jihar Anambra ta rike wata Virginia James, mai shekaru 39 a kan kudaden asibiti.

Punch Metro ta gano yadda asibitin ke rike da matar sakamakon yadda ta gaza biyan N248,000 da asibitin suke bin ta bashi.

Matar 'yar asalin Izzi ce, jihar Ebonyi, amma tana zaune a Ifiteisu Awka. Matar ta ce jaririnta ya rasu a asibitin bayan ta fuskanci wahalhalu wurin haihuwa.

James ta roki gwamnan jiharta ta asali, David Umahi, da dan uwansa, Willie Obiano na jihar Anambra, da kuma duk wasu mutanen kirki, da su taimaka mata ta biya wannan bashi.

Hukumar asibiti ta damke matar makaho a kan kasa biyan N248,000
Hukumar asibiti ta damke matar makaho a kan kasa biyan N248,000. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: Rikicin kudancin Kaduna ya dade yana faruwa, Sheikh Gumi

Ta ce, "Na shiga uku, bani da wani mataimaki a duniyar nan. Mijina ba shi da lafiya, ya kurumce kuma ya makance. Ni nake ciyar da shi da yarana 4, mata 3 da namiji 1.

"Ina sarar ciyawa, da dan wannan kudin nake rayuwa. Na zo da sunan haihuwa, bayan na haihu aka samu wata matsala.

"Bayan likitan ya ga halin da nake ciki, bai tambayeni kudi ba, sai yace ya kamata a yi min aiki. Amma yaron ya jigata, ya kusa mutuwa a lokacin, daga bisani ya mutu.

"Yanzu haka watanni 2 kenan da makonni 3 ina zaune a asibitin, bayan na haihu. Babu wanda yake kawomin ziyara. Asibitin ne suke ciyar dani.

KU KARANTA: Ban taba karbar albashi ba tun bayan hawa na kujerar gwamna, Gwamnan APGA

"Babbar matsala ta yanzu ita ce, ina bukatar in fita daga asibitin don in cigaba da 'yan ayyuka na, kafin yara na da miji na su mutu saboda yunwa."

Wani likita dake asibitin, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya kwatanta al'amarin a matsayin babbar matsala.

Kamar yadda yace, "mun yi mata aikin ne don mu ceci rayuwarta, shiyasa ba mu bukaci ta bamu ko sisi ba."

A wani labari na daban, wani Smart Odojie Ofagba, wanda 'yan sanda suka yi sanadiyyar kisan mahaifinsa, Samuel Udojie Ofagba, kawunsa, Abulimen Ofgba da leburan mahaifinsa, Kinsley, yana bukatar gwamnatin tarayya ta biya shi naira miliyan 50.

Ya sanar da wannan bukatar tashi ne yayin sanar da kwamitin bincike a kan wadanda jami'an SARS suka cutar da sauran makamantan laifuka.

Yace wani DPO ne ya kashe masa 'yan uwa a ranar 9 ga watan Maris ta 1999, DPO din shine Aisabor da ke karamar hukumar Usenu Irrua a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel