Sabuwar Shekara: El-Rufai Ya Yi Wa Fursunoni 11 Afuwa, Ya Tiki Rawar ‘Buga’ a Wajen Taro

Sabuwar Shekara: El-Rufai Ya Yi Wa Fursunoni 11 Afuwa, Ya Tiki Rawar ‘Buga’ a Wajen Taro

  • Gwamna Nasir El-Rufai ya yi wa fursunoni 11 afuwa a jiharsa domin bikin sabuwar shekara ta 2023
  • El-rufai ya yi hakan ne bisa shawarar da kwamitin jin kai na jihar ya basa na sakin wasu daga cikin fursononi
  • Gwamnan ya kuma taka rawar 'Buga' a bikin shiga sabuwar shekara na karshe da zai yi a matsayin gwamnan Kaduna

Kaduna - Yayin bikin shiga sabuwar shekara gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi afuwa ga fursunoni 11 da aka yankewa hukunci daban-daban a magarkamar Kaduna.

Gwamnan ya amince da afuwar nasu ne bisa tanadin Sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima wanda ya bai wa Gwamnan ikon yafewa mai laifi, jaridar Premium Times ta rahoto.

Gwamna El-Rufai
Sabuwar Shekara: El-Rufai Ya Yi Wa Fursunoni 11 Afuwa, Ya Tiki Rawar ‘Buga’ a Wajen Taro Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wani jawabi daga gidan Sir Kashim ya ce gwamnan, wanda ya yi aiki kan kwamitin jin kai na jihar, ya saki fursunonin a ranar Lahadi, 1 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Tsagin Atiku Abubakar Ya Fadi Gaskiya Game da Babban Asirin da Wike Ya Bankado Kan Zaben 2003

Jawabin ya kara da cewar wannan karamci ne na nuna tausayawa a ranar sabuwar shekara ta hanyar yin afuwa ga fursunonin da suka cancanta a cikin jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Fursunonin da suka ci gajiyar wannan shirin

Kwamitin jin kai na jihar Kaduna ya bayar da shawarar yin afkuwa tare da gaggauta sakin Musa John, Yakubu Abdullahi da kuma Habu Usman.

Sauran wadanda aka saki sune: Shamsu Usman, Abdullahi Abdulmumuni, Mahadi Abdullahi, Futune Mabuke, Abdullahi Lawal, Sunday Iliya, Mohammed Anas da Kayode Gabriel Adenji.

Kwamitin jin kan na jihar Kaduna a shirin afuwa ya bayar da shawarwari kan fursunonin da aka yankewa hukuncin shekaru uku ko wadanda ke da watanni shida.

"Dole ya kasance hukuncin da aka yanke masu bai fi watanni shida ba da fursunoni masu dogon zango wadanda suka fara shekaru goma ko fiye da haka a hukunci da aka yanke masu da masu fama da ciwon da ka iya kai ga mutuwa."

Kara karanta wannan

Ganduje: Dalilin Da Yasa Arewa Ba Ta Da Wani Uzuri Sai Dai Ta Zabi Tinubu

El-Rufai ya sha rawar Buga a bikin sabuwar shekara

Da farko, Malam El-Rufai ya yi godiya ga mutanen jihar kan damar da suka bashi na yi masu aiki, da kuma fahimta da goyon bayan da suka bashi tsawon shekaru.

Gwamnan wanda ya yi jawabi a bikin shiga sabuwar shekara da kungiyar KCTA ta shirya ya yi wa mutanen murnar shiga sabuwar shekara sannan ya roke su da kada su yanke kauna duk da mawuyacin hali da ake ciki.

Ya kuma bukace su da su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasar yana mai fatan cewa kokarin da aka yi a jihar tun daga 2015 na inganta rayuka zai ci gaba a gwamnatin gaba.

Ya kuma sanar da taron jama'ar cewa wannan shine bikin sabuwar shekara na karshe da zai yi a matsayin gwamna, yayin da ya yi masu bankwana.

Ya kuma yiwa dandagon jama'ar da suka taru rawar 'Buga' na bankwana kafin ya sauka daga mumbarin yana mai dagawa mutanen hannu.

A wani labari na daban, mutane da dama a soshiyal midiya sun jinjinawa wani matashi dan Najeriya bayan ya kera motar G-Wagon da hannunsa sannan ya hau ya karade gari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng