Babu Wanda Muka Yiwa Alkawarin Karin Albashi, Alawus Kadai Muka ce Zamu Kara: Ngige

Babu Wanda Muka Yiwa Alkawarin Karin Albashi, Alawus Kadai Muka ce Zamu Kara: Ngige

  • Gwamnatin tarayya ta yi fashin baki kan maganar alkawarin yiwa ma'aikanta karin albashi a sabon shekara
  • Rahotanni sun gabata cewa ministan kwadago ya ce ma'aikata su shirya, zasu sha karin albashi bana
  • Ngige ya ce shi dai ba haka ya fada ba karya yan jarida suka yi masa, alawus kawai zasu kara

Abuja - Ministan Kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige, ya karyata rahotannin cewa gwamnatin tarayya na shirin yiwa ma'aikatan gwamnati karin albashi a sabon shekara.

Ngige ya ce jawabin karin kudin da ya yiwa manema labarai a fadar shugaban kasa kawai na alawus din ma'aikatan gwamnati ne amma ba albashi ba.

Ministan ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar ta hannun shugaban sashen hulda da jama'a na ma'aikatar ayyuka, Mr Olajide Oshundun, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

Nigie
Babu Wanda Muka Yiwa Alkawarin Karin Albashi, Alawus Kadai Muka ce Zamu Kara: Ngige
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabin yace:

"Ministan Kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige, ya samu labarin da ke yawo a kafafen yada labarai cewa Gwamnatin tarayya na shawarar yiwa ma'aikatan gwamnati karin albashi bayan hirar da yayi da manema labaran fadar shugaban kasa bayan zamansa da shugaban kasa."
"Ministan na son bayyana cewa karin kudin da yake nufi kan alawus na ma'aikata, musamman na ma'aikatu."

Jawabin ya kara da cewa kwamitin fadar shugaban kasa kan albashi dake ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta samu shawari kan yin karin alawus ga ma'aikatun gwamnati da dama.

Yace:

"Ba albashi kwamitin ke shirin yin kari ba, maganar alawus akeyi kuma wasu kebabbun ma'aikatan gwamnati ne suka bukaci hakan."

Ministan Kwadago Yace Aiwatar Da Mafi Karancin Albashi Zai Taimaka Matuka Sosai

A wani labarin daban kuwa, batun mafi karancin albashi ya zama wani batu da aka kwashe shekaru ana tattaunawa a kai.

Kara karanta wannan

Buhari Na Tsaka Mai Wuya, Ƙungiyar Kwadugu Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Kan Abu 2

Shekara bayan shekaru, wasu jihohi har ila yau basu fara biyan ma'aikatanta mafi karancin albashin be.

Gwamnatin Tarayya ta kafa dokar cewa mafi karanci albashin da ya kamata a biya kowani ma'aikaci shine N33,000 a wata.

Ministan Kwadago, Dr Chris Ngige, ya ce idan jihohi zasu aiwatar da tsarin, ko shakka za'a samu ci gaba a Nigeria sosai da sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida